1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu:An kori shugaban hukumar karbar haraji

Abdourahamane Hassane
March 20, 2018

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya dakatar da aikin shugaban hukumar karbar haraji na kasar Tom Moyane.

https://p.dw.com/p/2uf9P
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa Hoto: Reuters/M. Hutchings

A cikin wata wasikar da shugaban na Afirka ta Kudu ya aike da ita zuwa ga Tom Moyane ya ce a karkashin jagorancinsa na hukumar, Afirka ta Kudu ta fada cikin wani hali na cin hanci. Tun farko  gwamnatin ta Afirka  ta Kudu ta bukaci shugaban hukumar karbar harajin da ya yi marabus amma ya yi kunan kashi.