Afirka ta Kudu tana fuskantar matsalolin tattalin arziki | Labarai | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu tana fuskantar matsalolin tattalin arziki

Ministan kudin Afirka ta Kudu ya ce kasar tana fuskantar lokaci mai tsauri tare da neman kara kudaden haraji

Ministan kudin kasar Afirka ta Kudu ya ce kasar tana fuskantar lokaci mai tsauri, kuma tilas sai an yi karin kudaden haraji, kafin gwamnati ta samu kudaden da take bukata wajen ayyukan ci-gaba.

Ministan Nhlanhla Nene wanda ya gabatar da kasafin kudi na tsakiyar shekara, ya rage karfin bunkasa tattalin arziki zuwa kashi 1.4 maimakon 2.7, kamar yadda aka za ta a watan Febrairu. Ministan ya ce matsalolin da ake samu a kasashen duniya suna shafar karfin tattalin arzikin kasar. Nene ya ce gwamnatin za ta kara tashi tsaye wajen yaki cin hanci da almubazzaranci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba