Afirka ta Kudu ta tsaurara matakan shige da fita saboda Ebola | Labarai | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu ta tsaurara matakan shige da fita saboda Ebola

Hukumomi ƙasar sun ba da sanarawar cewar sun hana matafiya 'yan ƙasashen Laberiya da Saliyio da Guinea shiga ƙasarsu saboda cutar Ebola.

Sanarwar gwamnatin ta ce 'yan ƙasar ta Afirka ta Kudu Kudu da ke zaune a cikin ƙasashen uku waɗanda ke da niyar komawa gida wannan doka ba ta shafesu ba, sai dai za su fuskanci bincike na musammun.

Kawo yanzu ƙungiyar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar ta Ebola ta kashe mutane 1350 a cikin ƙasashen yankin yammancin Afirka waɗanda suka haɗa da Saliyio da Laberiya da Guinea da kuma Najeriya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe