Afirka ta Kudu za a karbe filayen noma a ba bakar fata
August 1, 2018Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da cewa jam'iyyarsa ta ANC za ta bukaci yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran huska domin samun izinin karbe filayen noma daga hannun Turawa ba tare da biyan kudin diyya ba domin raba su ga al'ummar bakar fata masu rinjaye kana mafi talauci a kasar ta Afirka ta Kudu.
Ramaphosa ya sanar da wannan aniya tasa ce a wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin na kasar inda ya ce matakin zai taimaka ga bunkasar tattalin arzikin kasar.
A kasar ta Afirka ta Kudu dai, shekaru 24 bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata, fararan fata ne ke mallakar kaso 73 daga cikin dari na filayen noma masu albarka, filayen da gwamnatin ke son amfani da karfi a nan gaba domin karbe su da kuma rarraba su ga bakar fata a kasar.
Har ya zuwa wannan lokaci dai gwamnatin Afirka ta Kudu na sayen filayen ne daga hannun fararan fata domin raba wa bakar fata a kasar.