1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin biyan diyyar gonaki ya kunno kai a Afirka ta Kudu

Zulaiha Abubakar
November 30, 2018

Kotun daukaka kara a kasar Afirka ta Kudu ta yi watsi da karar da wakilan manoma Turawa suka shigar kan aniyar shugaban kasar Cyril Ramaphosa ta kwace musu gonaki ba tare da biyan diyya ba.

https://p.dw.com/p/39D6o
Simbabwe Tabakernte
Hoto: AFP/Getty Images

Batun gonaki da filaye a kasar dai na daya daga cikin batutuwan da ke jan hankali a fadin kasar, wanda ta yi fama da rikicin wariyar launin fata. Shugaba Ramaphosa ya dauki alwashin mayar wa da al'ummar kasar bakar fata gonakin su da Turawan suka karbe. Ya sha wannan alawashin ne a lokacin da yake yakin neman zaben shugabancin kasar wacce matasanta ke fama da rashin aikin yi.

Jim kadan bayan korar wannan kara dai, wakilan fararen fatar masu lakabin AfriForum sun shaida wa manema labarai cewar ba za su lamunci wannan hukunci ba .