1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wasu sun kai hari Coci a Afirka ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 11, 2020

A Afirka ta Kudu an kawo karshen garkuwar da wasu 'yan bindiga suka yi da wasu mutane a Cocin Pentecostal da ke Zuurbekom a yammacin birnin Johannesburg.

https://p.dw.com/p/3fAcq
Südafrika  Johannesburg | Geiselnahme in einer Kirche
An kama wadanda suka yi garkuwa da mutane a Coci a Afirka ta KuduHoto: picture-alliance/AP Photo/South African Police Services

Kakakin rundunar 'yan sanda Vishnu Naidoo ne ya bayyana hakan, yayin wata hira da ya yi da manema labarai jim kadan bayan da jami'an tsaron suka tseratar da mutane kimanin 200 da 'yan bindigar suka ritsa da su a Cocin yana mai cewa: "Mun kame sama da mutane 41 da muke zargi da hannu a wannan harin, ciki kuwa har da wasu shida da aka kai asibiti bayan sun samu rauni ta hanyar harbin bindiga. Mun kuma samu makamai da suka hadar da manya da kananan bindigogi sama da 45."

Rahotanni na nuni da cewa cikin wadanda aka kama da kai wannan harin, har da wasu jami'an 'yan sanda da kuma jami'an rundunar gyaran tarbiyya ta kasar.