Afirka ta Kudu da Kenya sun dauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka ta Kudu da Kenya sun dauki hankalin jaridun Jamus

Rikicin siyasa a Afirka ta Kudu da Kenya sun dauki hankalin jaridun Jamus na wannan makon dai dai lokacin da shugaba Zuma ke fama da masu adawa da ma kiraye-kirayen ya yi murabus.

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi tsokaci kan siyasar kasar Afirka ta Kudu. Jaridar ta fara ne da cewa Shugaba Jacob Zuma ba ya son yin hannu riga da madufun iko duk da cewa kwanakinsa kidayayyu ne a matsayin shugaban kasar, amma saboda fargabar ka da a bincike sa dangane da cin hanci da rashawa yana ci gaba da kankane madafun iko. Shugaba Zuma ya soke jawabinsa na halin da kasa ke ciki, karon farko da hakan ta farun a Afirka ta Kudu.

Jaridar ta ce jawabin na halin da kasar ke ciki batu ne mai matukar muhimmanci wanda tun a 1994 shugaba da aka zaba ta hanyar demokaradiyya ke samun damar fadin alkiblar da kasar ta fuskanta da kuma irin ci-gaban da aka samu.

 

 

Dandano na mulkin kama karya inji jaridar Neues Deutschland a sharhin da ta rubuta kan siyasar kasar Kenya tana mai cewa tun bayan zaben da aka gudanar tsarin demokaradiyyar kasar ta Kenya ya shiga wani yanayi na rashin tabbas. Ta ce madugun 'yan adawa Raila Odinga ya rantsar da kanshi a matsayin shugaban kasa na al'umma, ita kuma gwamnatin Shugaba Uhuru Kenyatta ta rufe wasu gidajen telebijin masu zaman kansu.

Jaridar ta kara da cewa a kasa da mako guda Kenya ta shiga wani yanayi da ya yi hannun riga da kyakkyawan tsarin demokaradiyya da aka santa da shi. Jaridar ta ce ba kafafan yada labaru kawai suka shiga taskon gwammati ba, hatta 'yan siyasa na bangaren adawa suna tsare a kurkuku. Wannan halin da ake ciki a Kenya na zama wani tuni ga al'umar kasar na lokacin mulkin kama karya na zamanin mulkin shekara 24 na Shugaba Daniel Arap Moi da aya kawo karshe a 2002.

Daga rikicin siyasar kasar Kenya sai kuma wani rikicin da ya sake kunno kai a lardin Ituri na kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. A labarin da ta buga dangane da wannan batun jaridar Die Tageszeitung ta ce lardin Ituri da ke zama tsohon dandali na daya daga cikin munanan kisan gilla a lokacin yakin Kwango, yanzu ya sake fadawa cikin wani tashin hankali, inda mahukunta ke amfani da karfi fiye da kima kan masu bore. Jaridar ta ce 'yan sanda a kasar ta Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango na daukar matakan ba sani ba sabo don murkushe masu zanga-zanga, inda a ranar Litinin suka harbe mutum guda har lahira lokacin da suka tarwatsa masu bore a garin Bunia da ke arewa maso gabashin kasar. A cikin masu boren da suka toshe hanyoyi suna kone tayoyi akwai wadanda aka tilasta musu barin yankunansu sakamakon kisan gilla da ke faruwa a wasu kauyuka da ke lardin Ituri, da ke bukatar gwamnatin Kwango ta dauki mataki a kan sabon tashe-tashen hankula masu nasaba da sojojin sa kai. Akalla mutane 30 aka hallaka a kauyukan da ke lardi na Ituri a farkon watan nan na Fabrairu.