Afirka nahiya mai cike da tashe-tashen hankula | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 11.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka nahiya mai cike da tashe-tashen hankula

Mafi yawan jaridun Jamus a wannan mako sun maida hankalinsu ne ga rikice-rikicen yan tawaye a kasashen Afirka da dama.

Al'amuran da suka dauki hankali cikin jaridun Jamus a wannan mako game da nahiyar Afirka, sun shafi halin da nahiyar take ciki ne na kokarin warware matsalolinta na yan tawaye da tarurrukan neman sulhu dasu.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba halin da ake ciki a jamhuriyar democradiyar Kongo, inda kungiyar yan tawaye ta M23 take kokarin kawo karshen mulkin shugaban kasa Joseph Kabila a Kinshasa. Tun kafin a shiga kashi na biyu na tattaunawa tsakanin yan tawayen da gwamnati a birnin Kampala na Uganda, yan tawayen ranar Talata suka sanar da cewar don kashin kansu sun amince da shirin tsagaita bude wuta, inda ma janar sakataren kungiyar ta M23 yace kungiyarsa zata kiyaye wannan shiri da tayi, koda kuwa gwamnati bata amince dashi ba. Yace yan tawayen sun amince da haka ne bayan da kasashe masu makwabtaka da Kongo, suka yi mata alkawarin cewar zata shiga shawarwari kai tsaye da gwamnatin Kabila. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace yayin da yan tawayen suka amince da tsagaita bude wuta, kungiyar hade kan Afirka ta AU tana ci gaba da shirinta na tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa gabacin Kongo, kamar yadda kasashe makwabta suka nema.

Ansar Dine Kämpfer in Mali

Mayakan yan tawayen Mali

Wani rikicin da ya dauki hankalin jaridun na Jamus a wannan mako, shine na jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda jaridar Süddeutsche Zeitung tace duk da tattaunawa da ake gudanarwa tsakanin hadin gwiwar yan tawaye mai suna Seleka da gwmanatin shugaban kasa, Francois Bozize, amma yan tawaye sun nuna cewar ba zasu tsagaita ba har sai sun ga bayan mulkin shugaban. Yanzu haka dai mayakan yan tawayen ya rage masu misalin kilomita 160 ne su isa birnin Bangui, sun kuma maimaita bukatarsu a zauren taron dake gudana a Libreville na kasar Gabon cewar tilas ne shugaba Bozize ya sauka daga mukamin sa kafin su amince da duk wnai shiri na sulhu. Kungiyar yan tawaye ta Seleka tana zargin shugaban ne da laifin kasa cika alkawuran da yayi a shekara ta 2007 da 2011 game da shigar da mayakanta gaba dayan su a rundunar sojan jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

A watanni da dama na sararawa, a wannan mako an sake samun tashin sabon rikici tsakaninh yan tawayen da suka mamaye arewacin Mali da dakarun gwamnati. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace akwai alamun cewar yan tawayen tun dama can sun ja da baya ne domin su sake daura damarar yaki, a shirin su na tabatar da mulkin arewacin Mali, inda suka mamaye. To sai dai a bayan dauki ba dadi ranar Litininin, mayakan gwamnati sun dakatar da yan tawayen yan kungiyar AZAWAD da magoya bayan su yan kungiyar Ansar al-Dine. Jaridar tace wannan dai shine karon farko da ya zama wajii sojojin gwamnati suyi amfani da makamai kan yan tawayen, tun da suka mamaye arewacin Mali a watan Aprilu na bara.

Sudan Omar al-Baschir und Salva Kiir

Shugaban Sudan ta arewa Omar Hassan al-Bashir(dama) da shugaban Sudan ta kudu, Salva Kiir

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan karo ta duba rikicin dake tsakanin Sudan ta arewa ne da Sudan ta kudu inda ta maida hankalinta ga yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin shugaban Sudan ta kudu, Salva Kiir da takwaran aikinsa na arewa Omar Hassan al-Bashir bayan tattaunawa a Addis Ababa. Karkashin wannan yarjejeniya, kasashen biyu tare da taimakon kungiyar hadin kan Afirka, zasu kirkiro wani yanki a kan iyakokinsu mai tsawon kilomita 2000 da ba zai kasance da sojojin ko wacce daga cikinsu ba, kamar yadda manzon sulhu na AU, Thabo Mbeki ya nunar a karshen tattaunawar. Sudan ta arewa da Sudan ta kudu suna fama da rikici tsakanihjn su a game da neman mallakar yankunan na iyaka dake da arzikin man fetur, wanda ma'adini ne da gaba daya suka dogara dashi domin rayuwarsu.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman