1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: Ana garaje da coronavirus

February 5, 2020

Wani babban jami'i a fannin kare yaduwar cututtuka a kasashen Afirka, ya koka kan yadda kasashen ke sakaci game da ware wadanda ake zargin suna dauke da kwayoyin cuta.

https://p.dw.com/p/3XHcd
Äthiopien Coronavirus l Flughafen - Ankunft
Hoto: DW/G. Tedla

Wani babban jami'i a fannin kare yaduwar cututtuka a kasashen Afirka, ya koka kan yadda kasashen nahiyar ke sakaci game da batun killace wadanda ake zargin suna dauke da kwayoyin cuta, musamman ma yanzu da hankalin duniya ke kan cutar coronavirus.

Jami'in, John Nkengasong, na kokawa ne musamman ta la'akari da bambance-bambance da ake da su na matakan kula da lafiya a nahiyar, yana mai cewa hakan zai janyo matsala wajen yaki da cututtuka.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai wani jirgi dauke da dalibai 167 daga China ya sauka a kasar Moroko, inda hukumomi suka ce za a killace su na tsawon kwanaki 20.

A birnin Legas babbar cibiyar kasuwancin Najeriya kuwa hukumomin ne ke shaida wa wadanda ke shiga kasar daga China, da su killace kansu da kansu, ta hanyar kiyaye hulda da 'yan uwa da abokai tare da mai da hankali kan alamun cutar ta coronavirus.

A baya-bayan nan ne kuwa Sudan ta Kudu, daya daga cikin kasashen duniya da bangarenta na lafiya ke da matukar nakasu, ta samar da na'urorin gwada zafin jiki a babban filin jiragen kasar da ke a Juba.