Afirka: Aikin hakar ma′adanai na barin baya da kura | Zamantakewa | DW | 03.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Afirka: Aikin hakar ma'adanai na barin baya da kura

Garuruwan Afirka da dama da suka yi tashen arziki lokacin aikin hakar ma'adanai na fadawa mawuyacin hali na talauci da lalacewar muhalli lokacin da aikin ya kawo karshe.

A kasashen Nahiyar Afirka da dama, garuruwan yankunan da ke da arzikin karkashin kasa na yin tashen a fannin harakokin arziki a lokacin da ake aikin hakar ma'adanan a cikinsu. To sai dai so tari da zaran aikin ya kare ko ya dakata a bisa wasu dalillai, wadannan garuruwa da al'ummominsu na komawa abin tausayi. Birnin Kipushi na jamhuriyar Demokradiyyar Kwango na daga cikin biranen da suka tsinci kansu a irin wannan yanayi. 

Birnin Kipushi na Kudancin yankin Katanga a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, birni ne da ya jima yana tashen harakokin arziki a sakamakon arzikin karkashin kasar da Allah ya huwace wa yankin inda aka kwashe shekaru ana hakar ma'adanai da dama da suka hada da bakin karfe da na karfen tutiya wato Zinc  da kobalt da dai sauran ma'adanan karkashin kasa. Kamfanin Gecamine da ya yi aiki hakar ma'adanan ya samar da guraban aiki dubu 33 ga al'ummar yankin wadanda suka share shekaru suna rayuwar mutunci ta la'akari da yadda kamfanin ke daukar nauyin karatun da na kiwon lafiyar ma'aikatansa da iyalansu a duk tsawon shekarun 1980. To sai dai a farkon shekaru 1990 a sakamakon faduwar darajar farashin bakin karfe a kasuwannin duniya da ma kuma tabargazar da shugabannin da suka jagoranci aiki suka yi ta aikatawa sun yi sanadiyyar durkushewar kamfanin tare da jefa al'ummar yankin a cikin halin ni 'iyasu. Alexi wani tsohon ma'aikacin kamfanin na Gecamine da yanzu ke zaman kashe wando:

Ya ce "Hatta samun dan abin da zan ci tare da iyalina a yau wahala ne, ta kai ni dole a yau ga zuwa yo itace ko kuma tsintar 'ya'yan itatuwa a daji in zo gari in saida"

  

Akasarin al'ummar birnin na Kipushi dai na fama da talauci a sakamakon rashin aikin yi wanda ya kai koluluwarsa a yau in ji Joseph Kabeya wani mazaunin birnin:

Ya ce "Muna shan bakar wahala, wasunmu sun mutu a sakamakon wannan wahala. Ni dinnan alal misali ina da yara 15 ban iya cida su ba kuma ban san inda zan shiga ba"

Wannan matsala ta rashin aikin yi dai a birnin na Kipushi ta yi sanadiyyar tabarbarewar harakokin tsaro da na zamantakewa inda sace-sace da sauran miyagun ayyuka suka yadu a cikin birnin da kewayensa. Bugu da kari an bar yankin da manyan ramuka da kura musamman a sakamakon yadda wasu mazauna yankin suka koma aikin binciken ma'adanin ta hanyar gargajiya da kwadayin samun na saka baki salati dan rage kaifin talaucin da ya yi masu katutu.