Afirka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus a wannan makon sun yi tsokacin kan boren sojoji a Cote d'Ivoire da manufofin Faransa a karkashin sabon shugaba kasar Emmanuel Macron da sake bayyanar cutar Ebola a kasar Janhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Elfenbeinküste Soldatenmeuterei (Getty Images/AFP/I. Sanogo)

Hukumomi a Cote d'Ivoire na ta fadi tashi wajen ganin ba a sake samun boren sojoji ba a kasar

A labarin da ta rubuta mai taken "Shugaba Ouattara ya gamu da fushin wadanda suka mara masa baya" jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi bayanin rikicin sojojin bore da ya barke a tun a Juma'ar makon daya gabata da irin barna da aka yi har da asarar rayuka. Tun a Juma'ar ce dai sojojin boren wadanda ke zama na tawaye da suka yi gwagwarmayar dora shugaba Alassane Ouattara kan karagar mulki suka yi gangami na nuna rashin jin dadinsu da gwamnati wadda ta ki biyansu alawus dinsu. Sojojin dai sun mamaye garuwa biyu mafi girma a kasar ta Cote d'Ivoire wato Abidjan da Bouake amma daga bisani an samu daidaitawa inda aka yi alkawarin share musu hawaye bisa sharadin su kuma za dakatar da tada kayar baya.

Frankreich Emmanuel Macron (Reuters/L. Bonaventure)

Kafafen yada labarai a Afirka na maida hankali kan Macron musamman ma manufofinsa a nahiyar

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland tsokaci ta yi dangane da yadda hankalin kafofin yada labaru da al'ummar kasashen Afirka masu magana da harshen Faransanci  kan zaben kasar Faransa. Shekaru kusan 60 bayan samun 'yancin kai daga mulkin mallaka, har yanzu siyasar kasar Faransa na da tasiri sosai a kan kasashen Afirka da ta mulka. Zaben Faransan dai ya kasancen labarun da gidajen talabijin da jaridu da Rediyoyi suka yi ta bibiya. Alal misali wata daliba 'yar kasar Senegal Fatou Faye wadda bata taba barin kasarta ta haihuwa ba, ta tambayi abokiyarta ta Faransa wanda ta ke goyon baya? Domin iata kan Emmanuel Macron ta ke so, a yayin da mahaifinta ya ke son Fillon.

ARCHIV Ebola-Ausbruch in Liberia 2014 (picture alliance/AP Photo/A. Dulleh)

Sake bullar cutar Ebola a Kongo ya sanya kasashe da dama jan damara don kare bayyanar cutar a kasashensu

Daga batun siyasa sai kuma na kiwon lafiya, inda aka sake samun bullar cutar Ebola a nahiyar Afirka musaman ma a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo. A sharhin da ta wallafa mai taken "gwamnatin kasar Kongo ta tabbatar da bullar cutar Ebola" jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce a  yankin arewa maso gabashin Janhuriyar Demokradiyyar Kongo, an samu bullar cutar Ebola. Kawo yanzu dai mutane 3 ne aka tabbatar da mutuwarsu a garin Bas-Uele, yankin da Ebolar ta bulla. A jimlace dai mutane 9 ne suka kamu da cutar. Sai dai ministan kiwon lafiya na Kongo Oly IIunga Kalenga ya yi kira ga al'ummar kasar da su kwantar da hanakalinsu domin gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace na shawon kan lamarin.