Afirka a Jaridun Jamus: 31.07.2020 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 31.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus: 31.07.2020

Dambarwar siyasar kasar Mali da karuwar coronavirus da kuma zanga-zangar wariyar launin fata da ta yadu a Afirka, na ci gaba da daukar hankulan jaridun na Jamus.

Mali | Präsident Ibrahim Boubacar Keita (Getty Images/AFP/L. Marin)

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita cikin tsaka mai wuya

A labarin da ta buga kan rikicin siyasar na Mali, jaridar Die Tageszeitung ta ce Imam Mahmoud Dicko da ke zama jagoran masu zanga-zangar adawa da gwamnati, ya yi nasarar kafa wata kungiya mai karfin gaske da ke jan hankalin dubun-dubatar mutane da a kullum suke amsa kiransa na fantsama kan tituna domin yin zanga-zanga. Jaridar ta ce kungiyar M5 da ta hada kungiyoyin farar hula da wani bangare na 'yan adawa ta shafe makonni tana zanga-zanga a Bamako babban birnin kasar Mali, lamarin da ya sa a dole gwamnatin shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita ta fara neman hanyoyin sulhu.

Sai dai ga Shugaba Keita da takwarorinsa na yammacin Afirka da ke kai gwauro suna kai mari da nufin yin sulhu, bukatar da masu zanga-zangar suka gabatar ta yi yi murabus ba abin karbuwa ba ce. Sau biyu tawagar kungiyar ECOWAS na zuwa Bamako domin ganawa da bangarorin biyu. A ranar Alhamis shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Cote d'Ivoire da Ghana da Senegal sun tafi Bamako, sannan a ranar Litinin da ta gabata, shugabannin kasashen kungiyar 15 sun yi taro ta kafar bidiyo a kan rikicin Mali, amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba. A ranar uku ga watan Agusta, 'yan adawa a Mali za su koma gudanar da zanga-zanga.

Süfafrika Johannesburg | Covid-19 Impfstoff Tests beginnen (picture-alliance/AP Photo/S. Sibeko)

Karuwar masu corona a Afirka

Daga rikicin kasar Mali sai annobar coronavirus da ke kara yaduwa a kasashen duniya ciki kuwa har da na Afirka, kamar yadda jaridar Neue Zürcher Zeitun ta labarto. Jaridar ta ce nahiyar Afirka ta dauki tsawon lokaci a matsayin wadda annobar corona ba ta samu gindin zama sosai ba, idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi. Sai dai a yanzu yawan masu kamuwa da cutar na karuwa a wasu kasashen Afirka musamman a Afirka ta Kudu. Tun ba yau ba, masana ke fargabar cewar annobar za ta yadu sosai a Afirka kamar yadda take yi a wasu sassan duniya. Jaridar ta ce da yawa daga cikin ksashen Afirka sun yi amfani da watannin baya-bayan nan wajen shiryawa yaduwar cutar, sai dai a lokaci daya mafi akasarin kasashen Afirka ba su yi wani shirin ko-takwana domin tinkarar cutar ba.

Statue des französischen Generals Leclerc in Douala Kamerun (Getty Images/Three Lions/Hulton Archive)

Rusa mutum-mutumin Turawan mulkin mallaka a Afirka

Yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da bambancin launin fata, an lalata mutum-mutumi da dama a fadin duniya. A Afirka akwai mutum-mutumin tsofaffin Turawa 'yan mulkin mallaka da yawa, amma yanzu wani mai fafatuka dan kasar Kamaru André Blaise Essama ya mayar da rusa wadannan alamomi na 'yan mulkin mallaka sabon aikinshi. A labarin da ta buga dangane da wannan mai fafatuka, jaridar Die Welt ta ce a karo da dama André Essama wanda kwararre ne a sassaka da kuma zane-zane, yana shiga hannun 'yan sanda a Kamaru suna kuma ci shi tara saboda lalata wasu abubuwa da ke yin tuni da ta'asar 'yan mulkin mallakar a Afirka. Sai dai da yawan mazauna birnin Douala da ke zaman mahaifar mai fafatukar, suna yi masa kallon jarumi kuma abin koyi. Wasu daga cikinsu da ma wasu daga kasashen ketare na biyan tarar da ake cin sa.

Sauti da bidiyo akan labarin