1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
May 28, 2021

A wannan mako juyin mulki da sojoji suka yi a kasar Mali ya dauki hankalin jaridun Jamus a labarai da sharhunan da suka yi kan nahiyarmu ta Afirka.

https://p.dw.com/p/3u5jP
Mali Bamako | Massenkundgebung zur Feier des Putsches
Sojoji sun sake karbe iko a MaliHoto: Reuters/M. Keita

"Juyin mulki cikin juyin mulki," wannan shi ne taken sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi game da juyin mulkin kasar Mali tana mai cewa: 'Yan kasar Mali sun yi maraba da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Agustan shekarar 2020, sun fantsama kan tituna suna nuna farin cikinsu. Sai dai a wannan karo komai ya yi tsit, domin da yawa daga cikin al'ummar kasar sun farga cewa a tarihin Mali juyin mulkin sojoji bai taba sa abubuwa sun inganta ba, sai ma akasin haka. A ranar Litinin da yamma sojoji a Bamako babban birnin kasar suka kame shugaban kasa Bah N'Daw da Firaminista Moctar Ouane da ke jagorantar gwamnatin rikon kwarya, suka kai su wani sansanin sojoji. Bayan juyin mulkin da aka yi wa shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan bara ne dai, aka nada su wadannan mukamai.

Mali Präsident der Übergangsregierung Bah N'Daw
Sojoji sun tilasta shugaban Mali na riko Bah N'Daw yin murabusHoto: Präsidentschaft der Republik Mali

Ita ma jaridar Die Welt ta yi tsokaci kan juyin mulkin tana mai cewa karo na biyu cikin wata tara Mali ta shaida sabon juyin mulkin soja. Jaridar ta ce sojojin Jamus na rundunar Bundeswehr na kan gaba wajen horas da takwarorinsu na Mali, saboda haka kiran dakatar da aikin horo ya yi yawa a Jamus. Ta ce ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bayyanna batun da wani abin da bai dace ba, amma shugaban Faransa ya fito karara ya kira shi da juyin mulki wanda ba abin da zai karbu ba ne. Jaridar ta ce ga kasashen duniya abubuwan da ke faruwa a Mali wani bala'i ne, tana mai cewa gamayyar kasa da kasa na tallafawa Mali kwarai da gaske, amma daga bangaren Mali babu wani abin da ake gani musamman wajen daukar nauyin harkokin siyasar kasar.
Birnin Goma a cikin fargaba, kasa ta motsa mutane sun shiga rudu a cewar jaridar Die Tageszeitung tana mai mayar da hankali kan aman wuta da wani dutse a gabashin Kwango ke yi, abin da ya yi sanadiyyar rayukan mutane da haddasa barna. Ta ce hanyoyi sun tsage, gidaje sun rufta kan mutane a birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, bayan shafe kwanaki dutsen Nyiragongo na aman wuta. Mutane fiye da 30 sun mutu yayin da sama da dubu 20 suka rasa gidajensu sakamakon aman wutar da dutsen ya yi a karshen makon jiya. Ana fargabar cewa hayaki da toka daga dutsen, ka iya janyo cututtuka masu nasaba da numfashi. Dama dai gabashin Kwango musamman lardin Kivu na Arewa mai shalkwata a birnin Goma, na fama da rikice-rikice na 'yan tarzoma.

Kongo | Vulkanausbruch Nyiragongo
Aman wuta da dutse ya yi a Nyiragongo, ya tilasta dubban mutane yin kauraHoto: Guerchom Ndebo/AFP/Getty Images

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan makon gajeren labari ta buga game da barazanar yunwa a kasar Madagaska tana mai cewa: Majalisar Dinkin Duniya ta rasa kudin da za ta samar da taimakon da ake matukar bukata a Madagaska. Yanzu wani fari mafi muni cikin shekaru 40 ya farma kudancin tsibirin, ya kuma haddasa matsalar karancin abinci. Shekaru uku ke nan ba a sami ruwan sama a yankin da abin ya shafa ba.