Afghanistan na bukatan tallafin tsaro | Labarai | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afghanistan na bukatan tallafin tsaro

Tun bayan janyewar dakarun NATO daga Afghanistan tsaro ya fara tabarbare abin da ya sanya Jamus neman kara nata dakarun.

Adadin dakarun sojin Jamus da ke yaki a Afghanistan zai karu a karon farko bayan shekaru da dama, sakamakon rashin tsaron da 'yan kasar ke fama da shi a daidai wannan lokacin, majalisar zartarwar tarayyar Jamus din ta ce za ta kara yawan dakarun daga 850 zuwa 980, sai dai wannan sai ya sami amincewar majalisar dokokin Bundestag.

Yanayin tsaron Afghanistan ya tabarbare kwarai da gaske tun bayan janyewar dakarun kungiyar kawancen tsaron NATO a shekarar da ta gabata, shi ya sa ma da dama daga cikin kasashen da ke kawancen tsaron suka kara wa'adin janye dakarunsu sabanin wa'adin da aka sanya a baya.

A 'yan watannin baya-bayan nan, kungiyar Taliban ta karbi jagorancin birnin Kundus, birni mafi girma a mataki na biyu a Afghanistan, kuma wurin da dakarun Jamus suke da sansani mai girma. Wannan ya kasance babban nasara ga kungiyar tun shekara ta 2001