1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani bayan Taliban ta kafa gwamnati

Abdourahamane Hassane LMJ
September 9, 2021

Zanga-zanga ta barke a yammacin Afghanistan bayan da 'yan Taliban suka nada sabuwar gwamnati wacce galibi ta kunshi 'yan kabilar Pashto, kana babu mace ko daya a cikinta.

https://p.dw.com/p/4056s
Afghanistan | Videostatement der Taliban - Mullah Baradar Akhund soll Taliban leiten
Mullah Baradar Akhund mataimakin firaminsta a gwamnatin TalibanHoto: SOCIAL MEDIA/REUTERS

Amirka da kungiyar Tarayyar Turai da sauran kasashen duniya, sun mayar da martani a kan gwamnatin da suka kira ta wariya. An dai nada Mullah Mohammad Hasan Akhund a matsayin sabon firaminista da zai jagoranci gwamnatin, yayin da Abdul Ghani Baradar daya daga cikin wadanda suka kirkiro kungiyar tare da Mullah Umar aka ba shi matsayin mataimakin firaminista. An kuma nada Mullah Yaqub dan Mullah Umar matsayin ministan tsaro sai Sirajuddin Haqqani jagoran da ke kusa da kungiyar Al-Qa'ida a matsayin ministan cikin gida.

Karin Bayani: Sharhi kan abin da Taliban ke yi

Ko da ya ke kakakin sabuwar gwamnatin Zabihullah Mujahid ya ce gwamnatin ba ta cika ba tukuna, domin suna  tattauna batun fadada ta da sauran kabilu na sassa dabam-dabam. To amma zanga-zanga ta barke a birnin Kabul da kuma yankin tsakiyyar kasar, inda aka kashe wasu mutane biyu a Talatar wannan mako.

Afghanistan Kabul | Anti-Pakistan Proteste
Zanga-zanga a Afghanistan, bayan Taliban sun sanar da jami'an gwamnatinsuHoto: WANA/REUTERS

Shugaban Amirka Joe Biden ya ce sun damu matuka da rashin kasancewar sauran kabiulu da kuma mata a cikin gwamnatin, yayin da kungiyar Tarayyar Turai ta ce tana bin abin da ke faruwa sau da kafa domin daukar mataki a kan Afghanistan din kan tauye hakkokin kabilun kasar da kuma mata.

Karin Bayani:Afghanistan na cikin mawuyacin hali

Sake dawowar ofishin ministan  gana ukuba da azaba a sabuwar gwamnatin da a shekaru 1990 wanda ke rike da matsayin ya rika gasawa jama'a wuta a hannu, yanzu haka ya sanya fargaba a cikin zukatan 'yan Afghanistan da sauran kasashen duniya. Sai dai wani babban jami na gamnatin Chaina ya ce ba za a zargi 'yan Taliban din ba, har sai an ga zubinsu. Kungiyar 'yan jaridu ta kasar Afghanistan, ta ce 'yan Taliban  sun cafke 'yan jariudu 14 na kasashen waje na wani dan lokaci kafin daga baya a sake su. Wannan ne dai karo na farko da kungiyar ta Taliban take gamuwa da fushin jama'a da nuna kyama, sabannin zamanin baya da suka yi mulki.