AFCON: Wasu kasashen sun san makomarsu | Siyasa | DW | 20.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

AFCON: Wasu kasashen sun san makomarsu

A yayin da ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON a Kamaru, kasashe da dama ya zuwa yanzu sun san makomarsu a gasar.

Gasar cin kofin Afirka 2022 | Wasan Guinea-Bissau da Najeriya

Najeriya ce kasa daya tilo da ta kammala zagayen farko da maki tara a gasar AFCON

Kasashe da dama da suka hadar da Najeriya da Kamaru mai masaukin baki da Maroko da Masar da Senegal da Burkina Faso da Malawi da Gabon da Guinea dakuma Cape Verde, sun samu nasarar tsallakawa zuwa zagaye na biyu na gasar. Sai dai kuma har kawo yanzu akwai sauran kasashe da ba su kammala sanin makomar tasu ba. A hannu guda kasashe kamar Habasha, gasar ta bana ba ta yi musu armashi ba, domin kuwa tuni suka fara hada komatsansu domin komawa gida. 

A karon farko dai cikin tarihin gasar cin kofin Afrikan, masu horas da 'yan wasa 15 cikin 24 sun fito daga nahiyar. Daga cikin su akwai tsofaffin 'yan wasa da suka yi suna da wasu masu horaswa na kasashen Afirka da ke neman yin suna. Ga misali mai horas da 'yan wasan Senegal Aliou Cissé ya kasance tsohon dan wasan baya mai farin jini, kuma ya yi nasarar sauya sheka zuwa horaswa.

Najeriya na daga cikin kasashen Afirka da suke da mai horas da 'yan wasa 'yan kasa, domin kuwa Augustine Eguavoen ya maye gurbin Gernot Rohr na Jamus, a matsayin mai horas da 'yan wasan kasar. Amma Augustine Eguavoen ya san Super Eagles sosai. Wannan dai shi ne karo na uku da tsohon dan wasan na Najeriya wanda ya buga wasanni 49 tare da cin kwallo daya ya samu kansa a matsayin mai horas da 'yan wasan na Najeriya. 

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin