AFCON 2022: Osimhen na Najeriya ya kamu da corona | Labarai | DW | 30.12.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AFCON 2022: Osimhen na Najeriya ya kamu da corona

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dan wasan na gaba ya kammala shirin zuwa kasar Kamaru domin ya buga wa Najeriya wasa a gasar kwallon Kafar Afirka ta AFCON da aka tsara gudanarwa nan da kwanaki goma.

Dan wasan kwallon kafar Najeriya Victor Osimhen ya kebe kansa bayan da aka same shi da cutar corona a wannan Alhamis. kungiyar Napoli ta gasar Lig 'Seria A' ta kasar Italiya ta yi wannan shela, inda ta nunar da cewa dan wasan mai shekaru 23 ya katse hulda da sauran jama'a na wani lokaci don gudun yada cutar . 

Hakan dai na nufin cewa akwai yiwuwar Victor Osimhen ya kasa shiga gasar AFCON  a kan kari, alhali yana daya daga cikin 'yan wasan da za su iya cire wa Super eagles kitse a wuta.


 Sabon kamun da coronar ta yi masa da ke zama na biyu a gare shi na zuwa gab da a yi masa gwajin lafiya na karshe kafin ya tafi Afirka.