Adu′o′in tunawa da fasinjojin Germanwings | Labarai | DW | 17.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adu'o'in tunawa da fasinjojin Germanwings

Jamus na gudanar aduo'i domin tunawa da mutane kimani 150 da suka mutu a hatsarin da jirgin saman ƙasar Germanwings ya yi a makonnin da suka gabata a Faransa.

Adu o'in waɗanda ake gudanar da su a babbar majam'iar Dom ta Kolon sun sami hallarta shugaban ƙasar na Jamus Joachim Gauck da shugabar gamnatin Angela Merkel.
Da kuma wasu jami'an gwamnatin ƙasashen Faransa da Spain daga cikin waɗanda aka gayyata mutun dubu 1400 da sauran iyalen mamanta kusan 500.

An dai tsaurara tsaro a zagayen Cocin a jana'izar ta ƙasa wacce gidajen talabijan da dama na Jamus ke watsawa kai tsaye.