1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon ministan aikin gona na Najeriya ya zama shugaban AfDB

Yusuf Bala/ Thomas Möesh/ LMJMay 29, 2015

Bayan zaben tsohon ministan noma na Najeriya Akinwumi Adesina a matsayin shugaban bankin raya kasashen Afirka na AfDB, ya ce akwai bukatar samar da hasken wutar lantarki a nahiyar.

https://p.dw.com/p/1FZCu
Shugaban bankin raya kasashen Afirka AfDB Akinwumi Ayodeji Adesina
Shugaban bankin raya kasashen Afirka AfDB Akinwumi Ayodeji AdesinaHoto: DW/T. Mösch

Adesina ya bayyana cewa hakan ya zamo wajibi in har ana son kasashen Afirka su sami ci gaba wajen bunkasar masana'antu. A yayin zantawarsa da yi da Thomas Möesch shugaban sashin Hausa na DW ya bayyana hanyoyin da yake ganin cewa zasu iya kai kasashen na Afirka yin gogayya da sauran kasashen duniya . Mai shekaru 55 a duniya Adesina ya gaji Donald Kaberuka na kasar Ruwanda, wanda ya yi wa'adi biyu a wannan mukamin tun daga shekara ta 2005 zuwa yanzu bayan kammala zaben sabon shugaban bankin na AfDB.

Tsohon shugaban AfDB Donald Kaberuka
Tsohon shugaban AfDB Donald KaberukaHoto: Getty Images/C. Somodevilla

Tunkarar kalubalen da Afirka ke fuskanta

Adesina dai ya karbi wannan kujera a daidai lokacin da nahiyar Afirka ke fuskantan sauyi a fannoni da dama, inda fannin masana'antu ke samun koma baya. Acewar Adesina abu na farko da zai taimaka wajen ci gaban nahiyar ta Afirka na zama yadda za a samar da cibiyoyi da zasu samar da makamashi.

Ya ce: "Zanyi farinciki idan ya kasance muna da kananan cibiyoyi na samar da makamashi masu zaman kansu amma abun dubawa a nan shi ne kasashen na Afirka basa habaka a fannin masana'antu. Idan ka duba irin abin da masana'antun mu na Afirka ke bayarwa a tsakanin takwarorinsu na duniya zaka ga cewa abin yayi kasa. Misali a shekarar 1989 Afirka na da sama da kaso daya cikin 100 amma a yau ya sauka da digo hudu. A yankin Asiya abin ya daga daga sama da kaso takwas zuwa sama da kaso 34 cikin 100. A saboda haka Afirka ba ta ci gaba ta fannin masana'antu kuma makasudin hakan shi ne rashin makamashi. Makamashi shi ne komai kuma shi ne zai hada kasashen na Afirka da sauran kasuwanni na kasashen duniya ta kowanne fanni".

An dade ana ruwa kasa na shanyewa

Ba dai tun yanzu bane wannan banki na raya kasashen na Afirka ke zuwa da tsare-tsare dan ciyar da nahiyar gaba ba amma a lokuta da dama wasu tsare-tsaren na karewa kan takarda ne kawai. To ko a wannan lokaci Mista Adesina ya ce akwai matakin da zai dauka.

African Development Bank Group
African Development Bank GroupHoto: ADB

Ya ce: "A matsayina na shugaban bankin raya kasashen Afirka abunda nake da burin gani, shine ganin yadda bankin zai zamo mai fafutuka a harkokin zuba jari yadda hankalin bankin zai karkata kan abunda ake samarwa daga karshe, wato aga kwalliya na biyan kudin sabulu. Banki ba zai zauna kawai ya ce ai ya fitar da sababbin tsare-tsare ba, kuma kwamitin amintattu ya amince da shi. Kasancewar banki ne na raya kasashe dole ne aga menene aka samu na ci gaba bayan an zuba jari, wannan na daga cikin abubuwan da na sa a gaba ".

Adesina dai ya yi nasarar samun shugabancin na bankin AfDB ne bayan da aka yi zaben har zagaye shida, inda ya yi nasarar doke ministocin kudin Cape Verde da Chadi. Masu zaben sun hada da masu hannayen jari a bankin su 80 da shugabanin kasashen Afirka guda 54 da kuma wakilan wasu kasashe 26 da ba na Afirka ba. Mutane takwas ne dai suka yi takarar neman shugabancin bankin bunkasa kasashen Afirkan wato AfDB.