Addu′o′in makoki a Poland | Labarai | DW | 17.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Addu'o'in makoki a Poland

Dubban 'yan Poland suka halarci addu'o'i ga mutane da suka rasu a haɗarin jirgin saman makon jiya

default

Dubbannen jama'a suka halarci wurin addu'o'in

Dubban 'yan ƙasar Poland suka hallara a dandalin Pilsudski inda aka yi addu'o'i a bainar jama'a ga mutane 96 ciki har da shugaban ƙasa Lech Kaczynski da suka rasa rayukansu a wani haɗarin jirgin sama a makon da ya gabata. Sun yi shiru na mintoci biyu kafin a buga jiniya da kaɗa ƙararrawar coci. Duk da kasancewar dandalin ya cike maƙil da jama'a amma komai ya tafi salin-alim inda suka yi ta kaɗa tutar Poland mai launukan fari da ja ɗaure da baƙaƙen ƙyalluna na alamar makoki. A gobe Lahadi za' a yi jana'izar shugaban da matarsa. Shugabannin ƙasashen duniya za su halarci wurin jana'izar to amma gajimaren tokar da ya tirniƙe sararin samaniyar nahiyar Turai ka iya hana wasu tawagogin halartar jana'izar. Shi dai Kaczynski da manyan jam´in siyasa da na rundunar sojin ƙasar sun raya rayukansu ne a wannan haɗarin jirgin sama da ya auku a Rasha ranar Asabar ta makon jiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala