Adawa da manufofin gwamnatin Guinea | Siyasa | DW | 07.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Adawa da manufofin gwamnatin Guinea

Jam'iyyun adawa a kasar Guinea sun shirya babban gangamin siyasa da nufin tilasta shugaba Alpha Conde ya yi wa dokokin zaben kasar gyaran fuska kafin karshen wa'adin mulkinsa.

'Yan adawar dai na wannan matsin lamba ne domin ciwa gwamnatin da ke ci a yanzu birki a yunkurin da take yi na sake tsayar da Conde takara a zaben da zai gudana a bana. Watanni 18 jam'iyyun adawar Guinea suka kwashe suna kai goro da mari don ganin cewa bangaren gwamnati ya saurari koke-kokensu da idanun basira, saidai hakarsu ya gaza cimma ruwa a neman da suke yi na mahukuntan kasar su yi wa dokar da ta shafi zabe kwaskwarima. 'Yan adawar dai na neman a kafa hukumar zabe da za ta kunshi mambobi daga bangaren gwamnati dana adawa, sannan kuma a kafa kotun tsarin muki tare da sake gudanar da kidayar al'umma domin a tantance adadin 'yan Guinea da suka cancaci kada kuri'a. A ganinsu wannan ita ce hanya mafi dacewa ta gudanar da zaben shugaban kasa da na kananan hukumomi da zai samu karbuwa ga kowa da kowa a wannan shekara ta 2015 da muke ciki.

Alwashin ci gaba da gwagwarmaya

Guinea Wahl Wahlen Unruhen Polizei UFDG Conakry Flash-Galerie

Aboubakar Syyla da ke zama kakakin gamayyar jam'iyyun adawar kasar ta Guinea ya ce za su ci gaba da gagwarmaya har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi

"Wannan gangamin da muka shirya, somin tabi ne na matakan da muke shirin dauka idan gwamnati ta ci gaba da yin kunnen uwar shegu ga bukatanmu. Matukar dai Guinea ba ta zama kasa da gwamnati za ta mutunta dokoki da kuma kundin tsarin mulki ba, to za mu ci gaba da shirya gangami."

Sai dai kuma hukumomin na Guinea sun soki lamirin 'yan adawar kasar, inda suka kwatantasu da 'yan neman tayar da zaune tsaye. Ita dai Guinea ta saba fuskantar rikici da ba ya rasa nasaba da kabilanci da kuma siyasa. Kazalika Guinea da ke yankin yammacin Afirka na fama da kalubale a fannin kiwon lafiya, inda cutar Ebola ke lakume rayukan 'yan kasar. Saboda haka ne gwamnatin Alpha Conde take ganin cewa bai dace 'yan adawa su kara karaya a kan targade ba. A ganinta dai hanya mafi dacdewa ita ce amfani da majalisar dokoki wajen cimma biyan bukata. Sekou Oumar Camara, jogo ne a jam'iyar RPG da ke rike da madafun ikon Guinea.

Babu bukatar shirya gangami

"Bangaren adawa ba ya bukatar wani babban gangami idan aka yi la'akari da cewa kafofin da ake da su a kasar sun bashi damar bayyana matsayinsa na siyasa. Kun san cewa Guinea na karkashin dokar ta baci a fannin kiwon lafiya, kasancewar annobar Ebola na ci gaba da barna. Wannan gangamin zai iya sa a fada cikin wani halin da ba za a iya shawo kansa ba."

Ita dai gwamnatin ta Guinea na cikin halin gaba kura baya siyaki. Babbar kungiyar kwadagon kasar ta tsunduma cikin yajin aiki a farkon wannan makon, inda ta ke neman da a inganta halin rayuwar ma'aikata da kuma yanayin da suke gudanar da aiki. Sai dai kuma an soke wannan yajin aiki sakamakon cimma matsaya da bangarorin biyu suka yi, inda gwamnati ta amince ta yi wa ma'aikata karin kashi 40 cikin 100 na albashinsu. Jam'iyyun adawar kasar ta Guinea dai sun goyi bayan yajin aikin da kungiyar kwdagon ta kira kafin su kai ga cimma matsaya da gwamnatin.

Sauti da bidiyo akan labarin