Adawa da karin wa′adi kan bashin Girka | Labarai | DW | 19.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adawa da karin wa'adi kan bashin Girka

Jamus ta bayyana rashin amincewarta da karin wa'adi na watanni shidda da Girka ta nema daga masu bin ta bashi domin a cewarta wannan ba hanya ba ce mai bullewa.

Mai magana da yawun ministan harkokin kudin Jamus Wolfgang Schaeuble ce ya bayyana wannan rashin amince ta mahukuntan Berlin a wata sanarwa da ta fidda da sanyin safiyar wannan Alhamis din.

Sanarwar ta ce karin wa'adin ba zai amfana komai ba illa ma sabawa ka'idojin da ke tattare da shirin da aka rigaya aka yi tun ba yau ba kan bashin, kazalika bukatar da Girkan ta bada ta sabawa irin tsarin da aka amince da shi a taron da aka yi kan wannan batu ranar Litinin da ta gabata.