1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin 'yan gudun hijira masu zuwa Turai zai karu

Salissou BoukariSeptember 18, 2015

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya HCR, ta yi kira ga Tarayyar Turai da ta yi amfani da damar da take da ita a yanzu domin daidaita matsalolin dubban 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1GYhY
Hoto: Getty Images/J. Mitchell

Hukumar ta ce adadin 'yan gudun hijirar da ke kwararowa zuwa nan Turai zai karu nan gaba cikin 'yan kwanaki masu zuwa, kuma hanyoyin da 'yan gudun hijirar suke bi za su kara yawaita. A wani taron manema labarai da ya jagoranta, kakakin hukumar 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya Adrian Edwards, ya ce taron Hukumar Tarayyar Turai da zai gudana a ranar Laraba mai zuwa, zai kasance wata babbar dama ta nema wa wannan matsala mafita, inda ya ce wannan zaman taro zai kasance tamkar wata dama ta karshe, ganin yadda Tarayyar Turai ta kasa daukan matakai kan matsalar da tun farko ake iya ciyo kanta.