Action Aid ta zargi G8 da rashin cikwan alkawali | Labarai | DW | 30.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Action Aid ta zargi G8 da rashin cikwan alkawali

Ƙungiyar bada agaji ta Action Aid, ta bayyana sanarwa a game da tallafin da ƙasashe masu karfin tattalin arziki ke baiwa ƙasshe matalauta.

Action Aid ta yi suka da kakkaussar halshe ,ga ƙasashen G8 a game da rashin cikwan alƙawali.

Ƙungiyar ta bada misalin taron shekara da ta gabata a ƙasar Britania, inda su ka alƙawarta yafe bassukan da su ka tambayo ƙasashe 35 mafi talauci a dunia, da kuma ware ƙarin dalla milion dubu 50, don talafawa wannan ƙasashe su yaƙi talauci, a tsukin shekaru 4 masu zuwa.

Ya zuwa yanzu, babu ɗaya daga wannan alƙawura, da ƙasashen G8 su ka cika, inji Action Aid.

Bugu da ƙari a shekara ta 2006,taimakon raya ƙasa ya ragu da dalla milion dubu 6, idan a ka kwatanta da shekarun baya.

Kamin taron G8, da zai gudana a Heiligendamm a nan ƙasar Jamus, mako mai zuwa,Action Aid ta yi kira ga shugabanin ƙasashe 8 mafi arziki a dunia,da su kasance masu cikwan alƙawali.