Accra da Abidjan sun tsaida farashin Cocoa | Labarai | DW | 12.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Accra da Abidjan sun tsaida farashin Cocoa

Kasashen Cote d'Ivoire da Ghana da ke zama kasashe biyu da suka fi noma Cocoa a duniya sun sanar da cewa daga yanzu ba za su sayar da Cocon ba kasa da Dalar Amirka dubu biyu da 600 kowane ton daya. 

Babban daraktan kamfanin Ghana Cocoa Board na kasar Ghana wato Joseph Boahen Aidoo ne ya sanar da wannan mataki a wannan Laraba a karshen wani taron kwanaki biyu da kasashen biyu suka yi a birnin Accra inda ya kara da cewa kasashen nasu za sun kuma dauki matakin dakatar da sayar da Cocon da za su noma a shekara ta 2020 da 2021 domin nazarin farashin da ya kamata su tsaida ga masu sayen Cocon da kasashen nasu ke nomawa. 

Tuni dai hukumomin kasashen guda biyu suka bayyana gamsuwarsu da wannan mataki da suka kira na tarihi.