Abzinawan Nijar ba sa son rikici irin na Mali | Zamantakewa | DW | 12.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Abzinawan Nijar ba sa son rikici irin na Mali

Duk da rashin gamsuwa da halin da suke ciki, Abzinawa da suka taɓa yin tawaye a arewacin Nijar ba sa sha'awar sake komawa fagen daga.

Rikicin tawaye da ake fama da shi a arewacin Mali, musamman na farkon wannan shekara, na barazanar bazuwa zuwa ƙasashen dake yankin wato kamar jamhuriyar Nijar, wadda a shekarun baya ta yi fama da rikicin 'yan tawayen Abzinawa, waɗanda sau biyu suna ƙaddamar da bore a lokaci guda da takwarorinsu na Mali. Ko da yake ba haka abin ya ke ba yanzu, amma gwamnatin Nijar da ma al'umar ƙasar na cikin fargaba.

Mohammed Kouda da ɗan uwansa Kola sun duƙufa wajen aikin gyaran lambunsu bayan wata ambaliyar ruwa da ta malala yankinsu. Waɗannan 'yan'uwan juna 'yan ƙabilar Abzinawa ne dake zaune a ƙauyen Iferouane a yankin Tuddan Air dake arewacin Nijar. Kouda na farbabar cewa idan aka sake yin ruwan sama to za su yi asarar albarkatun nomansu, kuma hakan ba zai kasance karo na farko ba. Da ƙyar ne dai ya yanke shawarar komawa aikin gona. Kouda mai shekatu 40 tsohon ɗan tawaye ne da ya yaƙi sojojin Nijar. Bayan shirin tsagaita wuta shekaru uku da suka wuce ya miƙa bindigarsa samfurin Kalashnikov. Sannan gwamnati ta yi masa da ma sauran 'yan tawayen Abzinawa kimanin 4000 alƙawarin kyautata musu don yin rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana.

"Ina aiki a lambu na, shi ne kaɗai damar da nake da shi. Ba mu samu wani abu daga gwamnati ba bayan mun ajiye makamanmu. Kashi 90 cikin 100 na tsoffin mayaƙan ba su da komai. Muna dai rayuwar ne haka amma ba mu da komai ba."

Kouda bai gamsu da halin da yake ciki ba. Amma duk da haka bai ga wani alfanun sake ɗaukar makami don ta da zaune tsaye ba, domin ba ya canza komai. Yanzu haka dai tsohon ɗan tawayen na cikin fargaba cewa mutane a Nijar ka iya sake ɗaukar makami don yin tawaye.

"Hatsarin a bayyane yake. Nijar na makwabataka da ƙasashe dake fama da rikicin siyasa. A arewa akwai Libiya, ga matsalar Mali a yamma, sannan a kudu da ita akwai rikicin ƙungiyar Boko Haram a Najeriya. Hakika rikicin siyasa a maƙwabtanmu na yin tasiri a ƙasarmu. Tun bayan rikicin Libiya makamai sun yaɗu a nan, ka na iya sayen bindiga cikin sauƙi da araha. Ga matasa na zaman kashe wando. Dole gwamnatin Nijar ta gane wannan hatsarin amma ba ta komai."

A cikin kaɗe kaɗen gargajiya da na zamani mutane ke hallartar wani taron neman zaman lafiya da ci-gaba da ƙungiyar agaji ta NIjar wato HED Tamat ta kira a tsakiyar ƙauyen Iferouane. Kawo yanzu ƙungiyar ta shirya irin waɗannan taruka har guda 11 a manyan unguwannin Abzinawa dake arewacin Nijar. Mano Aghali shi ne shugaban ƙungiyar agajin wadda Jamus ke a jerin ƙasashen dake tallafa mata da kuɗi.

"Manufar shirya wannan taro shi ne ba ma son a maimaita wani tawayen Abzinawa kamar yadda ya faru a shekarar 2007 a Nijar. Muna son mu yi amfani da wannan haɗuwar domin ba da gudunmawa wajen kyautata makomarmu ba tare da wani faɗa ko rikici ba."

Aghali dai ya shiga cikin tawayen al'ummar arewacin Nijar na farko a shekarun 1990. Ya kasance shugaban ɓangaren siyasa na wannan tawaye. Daga baya ya nemi ƙarin ilimi a fannin kimiyyar tattalin arziki, kafin ya shiga siyasa kuma ya kasance ɗan majalisar dokoki na tsawon shekaru. A lokacin da Abzinawan Mali da Nijar suka sake ɗaukar makami a shekarar 2007, Aghali bai shiga yaƙin ba, kasancewa yanzu ya yi amannar cewa hanyoyin siyasa ne mafi dacewa wurin yin sulhu amma ba na soji ba.

Mawallafa: Bettina Rühle / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi