Abzinawa sun ɗage tattaunawarsu da gwamnatin Mali | Labarai | DW | 27.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abzinawa sun ɗage tattaunawarsu da gwamnatin Mali

'Yan tawayen Mali sun ce ba za su tattauna da gwamnati ba muddin ba ta mutunta alƙawuran da ta yi mu su a baya ba.

Kungiyoyin tawaye na Abzinawa, waɗanda suka fi ƙarfi a arewacin Mali sun sanar da cewa sun ɗage tattaunawarsu da gwamnatin ƙasar dake Bamako, abin da ake ganin zai kawo koma baya ga shirin samar da dawamammen sulhu.

Batun da ya fi ɗaukar hankali shi ne makomar arewacin Mali inda Abzinawan ke kira Azawad. 'Yan tawayen dai sun ce suna neman yankin Azawad ya sami ikon cin gashin kan shi, abin da ita kuma gwamnati a tsakiya ta ce ba zata amince da shi ba

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar, kamfanin dillancin Faransa na AFP ya rawaito cewa ƙungiyoyin da abun ya shafa sun ce ba za su tattauna da gwamnati ba saboda matsalolin da ake fuskanta wajen aiwatar da tanadin yarjejeniyar Wagadugu waɗanda ke da nasaba da rashin mutunta alƙawuran da gwamnati ta yi tun farko.

Wannan yarjejeniya ta Wagadugu dai ita ce ta kawo ƙarshen watanni 18 na rikicin Mali, ta kuma tanadi yin zaɓe a watan Yuli wanda ya ɗora Ibrahim Boubacar Keita kan madafun iko, kuma a ƙarƙashin wannan yarjejeniya, 'yan tawaye da gwamnati sun amince su tattauna su kuma kare mutuncin iyakokin ƙasa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman