Abuja: Shugaba Buhari na daf da komawa gida | Siyasa | DW | 12.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Abuja: Shugaba Buhari na daf da komawa gida

Bayan barinsa Tarrayar Najeriya da nufin hutu na magani, shugaban Tarrayar Najeriya da ke riko ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce ya na kara samun sauki kuma zai dawo cikin kasa a lokaci na kankani.

Babu dai zato ba kuma tsammani fadar gwamnatin kasar ta aiyyana wata ziyara ta shugaban Tarrayar Najeriyar da ke riko Farfesa Yemi Osinbajo ya zuwa birnin London  da nufin ganawa da shugaban kasar da ke jiyya can.
Duk da cewar dai ganawar ta kare cikin tsawon awa daya, amma ta dauki lokaci a tsakanin al’umma ta kasar da suka dauki tsawo na lokaci suna neman ji game da lafiya ta shugaban.
Osinbajon dai ya shaida wa manema labarai bayan dawowarsa Abuja cewar ganawar ta tabo batutuwa da daman gaske sannan kuma shugaban ya na samun kari na lafiya.

Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo (picture-alliance/dpa)

Yemi Osinbajo da Mohammadu Buhari

"Na farkon fari dai kamar yadda kuka sani naje ne domin in ganshi in ga yadda yake na sha magana da shi ta waya amma kuma na ga ya dace in ziyarce shi. Sannan kuma in bashi bayanin cigaban da ake samu a gida. Mun tattauna batutuwa da daman gaske ya na cikin yanayi mai kyau , ya na samun sauki a cikin sauki, sannan kuma bashi da matsala”.
Kalaman na Osinbajo dai daga dukkan alamu na iya kaiwa ga kara kwantar da hankula cikin kasar da kai ke a rabe a tsakanin masu tunanin shugaban ya kasa da kuma magoya baya na Buharin da ke ganin ana neman ture shi da karfi na hatsi.
Tuni dai aka fara hasashen rabuwar kai har a cikin jam’iyyar APC mai mulki da ma majalisun tarrayar na kasar game da batu na rashi na lafiya ta Buharin da ma tasirinsa a harkokin mulki.

Sauti da bidiyo akan labarin