Abuja: Shirin rufe babban filin jirgin sama | Siyasa | DW | 05.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Abuja: Shirin rufe babban filin jirgin sama

Gwamnatin Najeriya ta bada sanarwar wani sabon shirin rufe filin jirgin sama na Abuja daga ranar takwas ga watan Maris don yin aikin gyara da sake inganta harkokin sufurin sama.

Sai dai da ta kai ga shi kansa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari soke wata ziyarar da ya yi shirin kaiwa a jihar Bauchi da ke sashen arewacin kasar a makon karshe na shekarar 2016 sakamakon rashin kyawun yanayi a filin jirgin saman da ke jihar. Haka kuma ta kasance da dubban matafiya bukukuwan Kirismeti da sabuwar shekara cikin kasar, inda aka rika soke sauka da ma tashi na jiragen a manya da ma kanana na filayen jirgin da ke kasar.

Matsalar inganci dai na zaman ta kan gaba cikin barazanar da a halin yanzu ke fuskantar tashoshi da yawa a kasar da ko dai ke da hanyoyin sauka da na tashin ko kuma babu na'urori na tallafa wa tsarin a cikin kowane yanayi. Na baya baya a cikin jerin masu irin wannan matsalar dai na zaman babban filin jirgin saman da ke a Abuja da gwamnatin kasar ta ce tana shirin kulle shi na tsawon wasu makonni guda shida domin yin gyara.

Ministan kula da harkokin sufurin sama na Tarrayar Najeriyar Senator Hadi Sirika dai na zaman karamin ministan sufurin da ke kula da tashoshi na jiragen na sama da kuma ya ce "gyaran na zama na wajibi da nufin ceto filin daga barazanar tsayuwar lamuran da yake fuskanta yanzu".

Karkata akalar jiragen sama zuwa Kaduna

Tun daga ranar takwas ga watan Maris ne dai ake sa ran kulle tashar ta Abuja gaba daya domin sake aikin gyaran titin saukar da ya share shekaru 34 da kuma tuni ya kai ga fara tsattsagewa. Wani karamin hadarin jirgin fasinjan Air France da ya kai ga lalata fuffuken jirgin dai na zaman na kan gaba cikin hujjojin sake gyaran filin da ke zaman na kan gaba a hanyoyin shiga da ma fita cikin kasar.

Nigeria Flughafen Lagos Archivbild 2007 (Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images)

Filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas shi ne mafi girma a Najeriya

Akalla fasinjoji miliyan biyar ne dai ke amfani da filin jirgin saman na Nmandi Azikwe a shekara, abin kuma da ya mai da shi daya daga cikin mafiya tasiri ga kasar.

Gwamnatin kasar dai ta ce tana shiri na tabbatar da cikakke na tsaro ga sabon filin jirgin sama na Kaduna da zai maye gurbin na Abujar domin masu zirga-zirga ko dai zuwa ga Abujar ta sabon layin dogo da tituna ko ma masu niyyar kadawa zuwa wasu sassa na kasar.

Ya zuwa yanzun dai gwamnatin kasar ta bada amincewa ga masu bada kariya a filaye na jiragen daukar makamai irin na zamani da nufin bada kariya ko dai a bisa hanyar ta Kaduna ko ma duk wani filin jirgin saman da ke kasar. Duk da cewar dai babu hari a bisa wani filin jirgi, kokari na fitowar kasar daga annoba ta ta'addanci dai na zaman daya a cikin hujjojji na sauyin fasali na tsaron a cibiyoyi daban-daban na gwamnatin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin