1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abuchi tsohon dan tasha da ya kama sana'a

Mansul Bala bello/GATJanuary 20, 2016

Abuchi ya shafe shekaru yana gararamba a karkashin gadojin birnin Iko bayan da ya taso daga garinsu shekaru 12 da suka wuce, kafin ya rungumi sana'a

https://p.dw.com/p/1Hh9A
Karte Nigeria Nnewi Deutsch Englisch
Hoto: DW

A Lagos, wani tsohon dan tasha ko Area-boys ya yi nasarar rikidewa zuwa wani abin misali tsakanin matasa a fuskar kasuwanci. Ya shafe shekaru yana gararamba a karkashin gadojin birnin Iko bayan da ya taso daga garinsu shekaru 12 da suka wuce, kafin ya cire wa kansa kitse a wuta.


Shi dai wannan mutun mai suna Abuchi Mathew mai shekaru 39 ya kasance abin misali ga duk wanda ya kira kansa da sunan matashi sabili da hangen nesa da ya yi na ganin duniya ta isa jima ga kowa


"A yanzu haka dai cike nake da farin ciki saboda a lokacin da na shigo lagos rayuwata ba ta da kyau domin ina kwana a kan titi tare da dukkan dabi'u marasa kyau amma wannan kasuwanci da na bude da tallafin Ubangiji na sami wurin kwana da abubuwa da dama'.

Mr mathew dai a yanzu haka shi ne shugaban wani dan karamin kamfani da ya sanya wa suna Chosen Digital Studio and Stationaries inda yake daukar hoto da kuma sarrafa kayan ofis


A yayin da Mr Abuchi ke kan aiki ba ya ji ba ya gani domin a cewarsa babu abinchi ga rago na tambayeshi ko masu tallafa masa yana jin dadin aiki da su


"Kwarai da gaske Ubangiji na amfani da su ta nemo min kwastomomi inda nake cigaba da aikin da ya dace"

A lagos batu na 'yan Kungiyar OPC ko Area-Boys don tayar da fitina ba sabon labari ba ne inda suke kwace da rana tsaka. Mr Abuchi dai ya ba su shawara ta hakika


"Shawarata a garesu ita ce su sami abin yi na sana'a kamar yadda shugabanninmu na Coci ke fada na dogaro da kai ko da kuwa sana'ar sayar da ruwa ce"

A dangane da tallafa wa tsaffinsa kuwa yace babu Ja.

"Sosai ina taimakonsu har ma da makwabtana domin na san irin radadin rayuwa da na shiga a baya wanda yanzu Allah ya taimake ni ya kawo ni lagos"

To sai dai ko yaya sauran matasa dake aiki da Mr Abuchi ke tunanin rayuwa a lagos? Mr Chibuzu Benjamin cewa ya yi


"Babu shakka muna amfani da wannan damar ce kawai domin ta zama tsani zuwa gaba"

Bincike da DW ta gudanar ya nuna cewa matasan da ake kira Area-Boys 'yan kasa yawancin su a yanzu sun fantsama cikin gari suna karbar abun goro a hannun direbobi da kuma kafa shingaye ga bin wasu hanyoyi kebabbu mai makon tsayawa da digadigansu