Abubuwa 10 da ya dace a sani game da Bundesliga
Gasar Bundesliga za ta shiga kakarta karo na 56. Har yanzu kungiyar Bayern Munich ce ke zaman ja gaba. Amma akwai wasu abubuwa da ya kamata mutane su sani game da rukunin farko na kungiyoyin kwallon kafar Jamus.
Bayern na ci gaba da haskawa
Sau shida a jere Bayern Munich na daukar kambun gasar. Gaba daya sau 28 ke nan kambun na isa Munich, kungiyar ta kware a wasanni kuma tana da karfin tattalin arziki. Tana samun kasa da Euro miliyan 600 a duk shekara. An kiyasta kungiyar a kan kudi Euro miliyan 265. An kiyasta kudin da 'yan wasan ke samu da cewa ya kai Euro miliyan 845. Bayern ta kasance ja gaba.
Sababbin kungiyoyi a rukunin farko
Abin alfahari: A karshen 2017/18 kungiyar 1. FC Nürnberg ta samu tsallakawa zuwa rukuni na farko na Bundesliga, bayan tsahon shekaru hudu a rukuni na biyu. A karo na takwas a tarihin Bundesliga. Babu wata kungiya da ta samu wannan nasara. Ita ma kungiyar Fortuna Düsseldorf da ita ma ta tsallaka rukuni na farko. Karo na shida ke nan kungiyar ta Rhineland na samun wannan dama. Shin ko za su iya?
Sabuwar fasaha: Amfani da na'urar sauraron magana ga masu bayar da horo
Alkalan wasa na Bundesliga sun jima suna amfani da na'urar sauraron magana. A yanzu masu bayar da horo za su fara amfani da ita. Ko wace kungiya an amince mata amfani da wadannan na'urori guda uku kacal. Za a iya amfani da rahoton kokarin 'yan wasan kai tsaye. An kuma inganta yanayin kula da 'yan wasan da suka samu raunuka a yayin gasar.
Amfani da na'urar daukar hoton bidiyo bayan gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.
An gabatar da wannan na'ura tun a kakar wasanni ta 2017/18, sai dai babu wata nasara. Tana aiki a hankali ga rikitarwa, inda aka yi ta sukan lamirinta. Amma yanzu komai ya gyaru. Bayan samun nasarar amfani da na'urar a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka gudanar a Rasha. Muhimmin sauyi: Za a rinka nuna hoton talabijin da matakin da aka dauka a bidiyon, abubuwa za su kasance a bayyane.
Daukar hankalin 'yan kallo a Bundesliga
Wannan na nuni da yadda "Bundesliga ke daukar hankali": Filin wasa na kungiyar Dortmund na da girman daukar wajen tsaiwa 24.454, filin wasa mafi girma a Turai. In kungiyar BVB na wasa a gida, 'yan kallo na cika filin. Filayen wasan Bundesliga na birge 'yan kallo. Ana samu 'yan kallo 43.878 a 2017/18 a ko wane wasa. Sabuwar nasara ta zama kan gaba a Turai, fiye da Ingila (36.000) da Spain (27.000).
Bundesliga - Gida mai yalwar wajen tsayuwa
Har yanzu a Bundesliga akwai "tsofaffin wurin tsayuwa masu kyau" Da farko sun zama tilas, yanzu sun dade da bacewa a Ingila da Italiya ko Spain. Tikiti mai arha, ka kuma yi kallo cikin kwanciyar hankali da jin dadi zuciyarka na cike da walwala. A dalilin haka, duk shekara Bundesliga na samun daruruwan 'yan kallo daga Ingila da ke baro kasarsu ta kwallon kafa zuwa kasar da ake tsayuwa don kallo.
Mace a matsayin alkalin wasa
Babu alkalin wasa mace a gasar manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai. Bayan fadi tashi a rukuni na biyu da na uku, an amince da Bibiana Steinhaus mace ta farko da za ta yi alkalancin wasa a Bundesliga, a ranar 10.09. 2017 ta yi alkalancin wasa tsakanin Hertha BSC da Werder Bremen. Bayan wata guda ta yi alkalanci tsakanin Schalke da Mainz. (Hoto) Wasanta na farko. Ta yi alkalancin wasanni takwas.
Corentin Tolisso - dan wasa mafi tsada da aka saya a Bundesliga
A 2017 kungiyar Bayern Munich ta sayo dan wasan Faransa Corentin Tolisso a kan kudi Euro miliyan 41 da rabi. A tarihi ba a taba sayan danwasa mai tsada kamarsa a Bundesliga ba. Tolisso ya fi kudin da Bayern ta siyo Javi Martinez wanda ta saya Euro miliyan daya da rabi. Dan wasan Dortmund Ousmane Dembélé ne, dan wasa mafi tsada da Bundesliga ta sayar a 2017, a kan kudi sama da Euro miliyan 100.
Ba a kayyade yawan 'yan wasa daga kasashen ketare ba
Ba kamar Spain da Faransa ba, ba a kayyade adadin 'yan wasan da ba 'yan kungiyar EU da za su buga wasa a Bundesliga ba. Kungiyar Eintracht Frankfurt na da 'yan wasa daga kasashe daban-daban. A rana ta biyar a kakar wasanni ta 2017/18 Frankfurt ta je Kolon da 'yan wasa 11 daga kasashe 11. An yi canjin 'yan wasa Jamusawa Marco Russ da Marius Wolf. Sun kuma burge da samun nasara ta ci daya da nema.
Filin Schalke Arena - Filin Wasa, Wajen Bauta, Dakin Taro
Magoya baya da dama na kiran filin wasan kungiyoyinsu da wajen bauta. Ga Frankfurt da Berlin da kuma Schalke, ga kungiyoyin uku akwai kamshin gaskiya. A baki dayan kungiyoyin uku akwai wajen bautar Kiristoci. A hannu guda, filin Schalke Arena ne kadai filin wasa a Turai da ke da rufi a samansa. Filin wasa mai rufi, wanda a Bundesliga ne kadai ake da shi.