Abu Namu: Halin da ′yan gudun hijira a Borno da ke Najeriya suke ciki | Zamantakewa | DW | 23.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Abu Namu: Halin da 'yan gudun hijira a Borno da ke Najeriya suke ciki

'Yan gudun hijira musamman mata da kananan yara a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram ya daidaita na cikin halin tasku.

Rikicin na Boko Haram ya tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa gidajensu har kuma suka tsinci kansu a sansanonin 'yan gudun hijirar, suna fama da tarin matsaloli, kama daga na rashin abinci da sutura da matsugunni, har ma gagarumar matsala ta fyade. Rahotanni sun nunar da cewa wadanda suka tsinci kansu a sansanonin 'yan gudun hijirar na tsintar kansu cikin halin musgunawa da ya hadar da fyade. Ba wai mata da yara mata ne kawai ke gamuwa da ibtila'in na fyade ba, har ma da yara maza sai dai matsalar tafi kamari a kan mata.

Tuni dai kungiyoyin fararen hula a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriyar suka fara yin kira ga hukumomi a jihar Borno da su dauki matakan magance matsalar fyade a sansanonin 'yan gudun hijira a jihar, ganin cewa duk da matakan tsawatar da mahukuntan ke dauka na kare 'yan gudun hijirar, ana samun karuwar matsalar yi wa mata da yara fyade a sansanoninsu da ke Maiduguri fadar gwamnatin jihar ta Borno.

Wannan batun shi ne shirin a Abu Namu ya mayar hankali kai.

Sauti da bidiyo akan labarin