Abu Namu: Cin zarafin mata a shafukan intanet
January 14, 2019Talla
A shirin na wannan lokaci ya duba tarin kalubalai da cin zarafi da mata ke fuskanta a kafafen sadarwa na zamani. Wadannan kalubale dai sun hada da zagi da hantara da kalaman batanci da na batsa da barazana, kai a wasu lokutan ma matan kan hadu da wasu a kafafen sadarwar na zamani kama daga facebook da instagram da twitter da dai makamantansu, inda daga bisani su kan shirya haduwa inda matan kan fuskanci matsalar fyade ko ma kisa baki daya.