Abu na Mu (10.10.2018): Auren Sha′awa | Zamantakewa | DW | 15.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Abu na Mu (10.10.2018): Auren Sha'awa

Mun duba wani sabon samfurin aure mai lakabin "Auren sha'awa" a arewacin Najeriya, da farko dai namiji da mace ne za su hadu ba tare da binciken asali ba sai su yarda kan yin auren wani lokaci don biyan bukatun rai.

A baya dai ana yin wannan aure a boye yanzu har ya fara fitowa fili sakamakon yadda rikici yake ballewa da mutuwar wannan takaitaccen aure, Hajiya Hafsat Baba ita ce kwamishinar  hukumar kula da harkokin mata da kananan yara ta Jihar Kaduna Najeriya, ofishinta da ke zaman sansanin sauraron matsalolin iyali ta yi bayani kan irin matsalolin da wannan aure ke haifar wa mata, inda ta ce wani lokaci iyaye ne ke kwadayi sai a tura yarinya gidan aure ko da yarinyar ba ta taba ganin mijin ba.

Bincike ya nuna cewa shi fa wannan aure na sha'awa dama ana yi ne don wani buri kamar samun jari ko rabauta da zuwa wasu kasashen ko asiya wa mace mota ko kuma shi namijin ya auri mace mai kudi in za su rabu ta kawo wani abu ta yi masa ihisani ko don kyan halitta daga bangarorin  biyu.

Da ma dai wasu yankunan na arewacin Najeriyar sun jima da samun tambarin rauni wajen rikon aure kafin kara samun wannan dama mai kama da maye fake da agana, to amma ma'auratan sun ba da hanzarin cewar shifa wannan aure da ma sun deba masa wa'adi ne ba zama ne irin na hakuri da juna ba. Ga dai wata uwa kan wannan batu inda ta ce wasu mazan kan auri mace ko ta halin kaka don su kawar da sha'awarsu muddin suka yi abin da suke da buri sai su saki mace ba tare da la'akari da makomarta ba. Ko nawa ne irin mazan kan kashe su auri macen da zarar sun biya bukatarsu shike nan.

Wasu malaman dai na cewa wannan aure shedanci ne tsakanin al'umma, ba ga bangaren Musulmi ba, ba ga bangaren Kirista ba. Wani lokaci kuwa al'ummar unguwa na taka rawa wajen gyara ko rashin gyara.

 

Sauti da bidiyo akan labarin