Abiy Ahmed ya koma a fagen daga | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 26.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Abiy Ahmed ya koma a fagen daga

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan firaministan Habasha Abiy Ahmed da ya bar birnin Addis-Ababa zuwa fagen yakin da gwamnatinsa ke yi da mayakan Tigray masu fafutikar ballewa.

Äthiopien Tigray Konflikt l Gedenkgottesdienst für die Opfer mit Premier Abiy Ahmed Ali

Firaministan Habasha Abiy Ahmed

Mu fara da sharhin jaridar die Tageszeitung, wace labarin ta ya fara da cewa, "mutumin da ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel yanzu shi kansa yana fagen yaki." Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya bar Addis-Ababa zuwa fagen daga a yankin da suke yaki da mayakan Tigray. Bayan makwanni ana kai kawo ta bangaren masu shiga tsakani na kasa da kasa, inda aka bude kafar tattaunawa tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan Tigray, a yanzu komai ya kasance a banza. Domin a bisa sanarwar da gwammnanti ta fitar daga wannan Laraba Firaminista Abiy Ahmed baya zama Addis Ababa babbau birnin kasar amma ya koma bakin daga. Jaridar ta ruwaito kakakin gwamnatin Habasha Legesse Tulu na mai cewa, tun ranar Laraba Abiy yana jagorantar dakarun da ke yaki, inda yanzu aka mika ragamar tafiyar da mulki a hannu ministan harkokin waje wanda dama can shi ne mataimakin firaminista.

Matsalar tsaro ta hana karatu a Burkina Faso

Mauretanien G5 Sahel Taskforce

Sojan Burkina Faso a fagen yaki

Jaridar ta die Tageszeitung  ta yi labarinta kan rikicin kasar Burkina Faso, inda ta ce "tsoro ya hana a bayar da karatu". A yanzu haka kimanin makarantu 2600 ne suka rufe bawai don cutar corona ba, amma don yawaitan hare-hare da ‘yan ta'adda ke kai wa makarantu. Dubban daruruwan yara ne suka yi asaran karatu, inda matasa da yakakamata a ce suna cikin azuzuwa yanzu sai watangariri suke yi kan tituna. A yanzu iyayen da 'ya 'yansu sun cunkushe a sansanonin 'yan gudun hijira. Ga karancin abinci da kayan sawa, a takaice mummunan yanayin da 'yan gudun hijirar da suka tsallako daga garuruwansu ke ciki ba ya misaltuwa.

Zargin ADF da kai harin ta'addacin Kampala

Afrika Uganda Edward Katumba Wamala

Edward Katumba Wamala babban hafsan sojan Uganda

Gwamnatin Yuganda ta zargi 'yan tawayen ADF da ke zama a gabashin Kwango da alhakin harin bama-bamai wanda aka kai a Kampla babban birnin kasar ta Yuganda. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ita ce ta yi wannan labarin. Jaridar ta ce mayakan da suka fi hatsari a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango a yanzu sun hade da kungiyar IS. 'Yan tawayen ADF sun kaddamar da hari a makwafciyarsu Yuganda, inda suka jefa tsoro a zukatan al'ummar kasar. Bayan harin ta'addanci da aka kai a Kampala babban birnin kasar yanzu tsoro ya mamaye zukatan jama'a inda a shagunanan sayar da kaya, wuraren shan barasa da sauransu duk inda mutum zai shiga sai da taka tsantsan. Matasa basa iya rataya jakar baya don gudu kada ‘yan sanda su zargesu da zama masu tayarda bama-bamai.

Annobar coronavirus na barazana a Afirka ta Kudu

Südafrika Covid-19 Impfung in Soweto

Allurar corona a Afirka ta Kudu

Jaridar Der Tagesspiegel ta yi labarinta kan annobar corona inda ta ce da farko dai an yi hasashen nahiyar Afirka za ta gamu da bala'in corona. Jaridar ta ce da fari a kasashen Afirka an dauki matakan rufe kasuwanni da wuraren taruwar jama'a, amma kuma yanzu an sassauta dokokin da aka saka, an bar jama'a yin mu'amala a wurare kamar dakunan cin abinci da sayar da barasa, wannan kuwa na faruwa ne a nahiyar Afirka a ya yinda a can nahiyar Turai ake samun karuwar alkaluman wadanda suka kamu da cutar corona, wanda ta kai ake shirin sake yin kullen jama'a. Misali yanzu a kasar Afirka ta kudu wace ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da corona a nahiyar Afirka, ana samun ko wace rana mutane 500 da suka kamu, yayinda wannan adadin bai fi kashi daya na yawan alkaluman da ake samu daga kasar Jamus a rana guda.

Sauti da bidiyo akan labarin