Abidjan: Guillaume Soro ya nemi gafara | Labarai | DW | 21.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abidjan: Guillaume Soro ya nemi gafara

Shugaban majalisar dokokin kasar Cote d'Ivoir, kuma tsohon Firaminista Guillaume Soro, ya nemi gafarar 'yan kasar, yana mai cewa zai nemi gafara ga tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo domin hadin kan kasa

Soro ya yi wannan furuci ne a wani mataki na neman sasantawa da juna, inda ya ce hakan ba za ta samu ba sai kowa ya yafe wa juna. Shugaban na Majalisar dokokin kasar ta Cote d'Ivoir ya ce al'ummar kasar ta wahala sosai, kuma rabuwar kawuna ba za ta haifar da komai ba sai koma baya, don haka ya yi kira ga al'umma ta ko wane bangare da su yafe wa juna.

Guillaume Soro da ake wa kallon wanda yake da burin neman shugabancin kasar ta Cote d' Ivoire, ya ce nan da 'yan kwanaki masu zuwa zai kara matsa kaimi kan wannan mataki da ya dauka na ganin 'yan kasar sun yafe wa juna. Shi dai Soro ya kasance madugun 'yan tawayen arewacin kasar ta Cote d' Ivoir daga 2002 zuwa 2011, inda ya zama Firaminista bayan kawar da gwamnatin Laurent Gbagbo.