Abbas zai sanarda kuriar raba gardama a yankin Palasdinawa | Labarai | DW | 06.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abbas zai sanarda kuriar raba gardama a yankin Palasdinawa

Rahotanni daga yankin gabas ta tsakiya,sunce shugabanin kungiyar Hamas sunyi kira ga janyewa daga kuriar raba gardama da ake sa ran yau shugaba Mahmud Abbas zai sanya ranar gudanarwa,dangane da yarjejeniya tsakaninsu da Israila.

Biyowa bayan rashin cimma yarjejeniya tsakanin Abbas da Hamas dangane da shawarar Abbas din wadda ta hada da amincewa da kasancewar Israila,shugaban na Palasdinawa ya lashi takobin tabbatar da barazana da yayi na bada waadin kwanaki goma kafin ya kira a jefa kuriar raba gardama akan batun.

Ana dai sa ran cewa nan da wata guda ne zaa gudanar da kuriar ta raba gardama.

Sai dai wani minista gwamnatin Hamas Naif Rajoub yace kungiyar ta Hamas zata kira magoya bayanta da su janye daga kuriar raba gardamar akan amincewa da Israila tare da kin gyara manufofinta dangane da kasar Israila.