Abbas: Za′a iya cimma sulhu da Israila | Labarai | DW | 25.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abbas: Za'a iya cimma sulhu da Israila

Jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas yace ya yi imani za'a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra'ila.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya shaidawa mashawarcin fadar White house ta Amirka Jared Kushner yayin wata ganawa da suka yi cewa yana gani akwai dama ta samun sulhu tsakanin Falasdinawa da Israila.

"Muna maraba da tawagar Amirka karkashin jagorancin Jared Kushner domin farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Falasdinawa da Israila. Mun yi maraba da yunkurin na Trump wanda ya baiyana tun farko cewa zai samar da yarjejeniya mai karfi ta zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya."

Mahmud Abbas yace ko da yake al'amuran sun yi tsauri matuka amma ba'a fidda tsammanin samun masalaha ba.

Kushner wanda har ila yau suruki ne ga Trump ya baiyana wa shugaban Falasdinawan cewa shugaba Trump na cike da fatan jama'ar Falasdinawa da Israila za su zauna daura da juna cikin lumana da zaman lafiya da kwanciyar hankali.