1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abba Kyari, jigo a gwamnatin Shugaba Buhari ya rasu

April 18, 2020

Hukumomi a Abuja fadar gwamnatin Najeriya sun tabbatar da rasuwar shugaban ma'aikata na fadar Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Abba Kyari, bayan ya kamu da cutar Corona.

https://p.dw.com/p/3b6D9
Präsident Buhari steht dem FEC vor
Na uku daga hagu, shi ne marigayi Malam Abba KyariHoto: Noso Isioro

Babban jami'i mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ne ya sanar da wannan labarin a shafinsa na twitter a tsakar daren da ya gabata. Marigayi Malam Abba Kyari, wanda dan saba'una ne, ya kwanta jinyar cutar ta COIVD-19 ne a Legas kafin Allah Ya yi masa wa'adi, bayan komawa kasar daga Jamus da ma ziyarar da ya kai kasar Masar.

Fadar shugaban na Najeriya ta bayyana kaduwarta da rashin jami'in da ake ganin wani mai fada a ji ne daga cikin mukarraban Muhammadu Buhari a gwamnatin kasar. Malam Abba Kyari wanda da make da wasu matsaloli na lafiya, shi ne dai babban jami'i na farko da ya rasa ransa sanadin wannan annoba a nahiyar Afirka baki daya.

Cutar ta Corona ta kashe mutum 17 ke nan a Najeriyar, yayin da wasu 493 ke jinyarta.