1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben Gwamnan Kano

Nasir Salisu Zango ZUD/AH)
March 19, 2023

Engr. Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP ya lashe zaben gwamnan jihar Kano inda ya ka da abokin hamaiyarsa na APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna. Tuni dan takarar APC din ya yi wa sabon zababben gwamnan fatan alheri.

https://p.dw.com/p/4OuFt
Nigeria Abba Kabir Yusuf
Hoto: Sanusi Bature

A jihar Kano cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya dubban magoya bayan jam'iyyar NNPP ta tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun bazama tituna suna shagulgulan murnar lashe zaben gwamnan jihar. Jama'a da dama sun baiyana nasarar ta NNPP da cewa nasara ce ta al'ummar Kano baki daya sun kuma tunatar da shi da ya cika alkawuran da ya yi wa al’ummar jihar.

A jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad kuma dan takarar gwamnan Jihar Bauchi a karkashin lemar PDP, ya samu nasarar sake zama gwamnan Jihar bayan zaben da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Bala Mohammed gwamnan jihar Bauchi
Bala Mohammed gwamnan jihar BauchiHoto: Ubale Musa/DW

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, mukaddashin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, ya shaida cewar Bala Muhammad ya sami nasarar sake zama gwamnan Jihar Bauchi ne da kuri’u 525,280 da ya kayar da babban abokin hamaiyarsa na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar da ya sami kuri’u 432,272

A jihar Sokoto hukumar zabe ta bayyana Jam’iyyar APC mai adawa a jihar a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna, sai dai Jama’iyyar PDP mai mulki ta yi watsi da sakamakon ta na cewa zasu yi nazari kan sakamakon zabe. A jihar Kebbi kuwa hukumar zaben ta kasa INEC ta ce zaben gwamnan bai kammala ba.

Zaben Najeriya na 2023
Zaben Najeriya na 2023Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Hukumar zabe ta kasa a jihar Filato ta sanar da dan takarar jam'iyyar PDP Caleb Mufwan a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar bayan ya sami kuriu 525, 209 inda ya kada  abokin takarar sa Nantawe Yilwada na jam'iyyar  APC  wanda ya sami kuri'u 481, 370 

Daga jihar Nasarawa Engineer Abdullahi Sule na jam'iyyar APC yayi nasara inda ya kada abokin takararsa na jam'iyyar PDP.

A jihar Benue kuwa, jam'iyyar APC ce ta lashe zabeni, inda Rev. Father Hyacinth Alia, ya kada abokin takarar sa Titus Uba na jami'yyar  PDP  da  kuriu 473, 973, yayin da Titus Uba na jam'iyyar PDP  ya zami kuri'u 223, 913. 

A kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya sakamakon zabe ya fara fita a yankunan  Sai dai jahohin Rivers da na yankin Igbo kamar Enugu,da Abia ana ci gaba da tattara alkaluman sakamakon zaben da kuma fuskantar kalubalen wakilan Jam'iyyu a dakin zauren tattara sakamakon.