A Zamanin Baya – Tarihin Afirka | Learning by Ear | DW | 18.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

A Zamanin Baya – Tarihin Afirka

Afirka ce tushen ɗan Adam. Ta ƙunshi manyan dauloli sannan tayi asarar dubban dubatar 'ya'yanta sakamakon cinikin bayi. Sai ku zo mu kewaya cikin tarihinta mai ban al'ajabi.

default

A wata fuskar dukkan mutane 'yan Afirka ne. A wannan nahiya ce 'yan Adam suka fara rayuwa. Ƙarnuka da dama bayan haka aka samu manyan dauloli a sassa daban-daban na nahiyar. Amma kuma, daidai da sauran nahiyoyi, ita ma Afirka tana da tabo a tarihinta. Misali dai cinikin bayi ko kuma mulkin mallaka na Turawa.

Sai a biyo mu wajen waiwayar tarihin Afirka da kuma darussan da za a iya koya domin kyautata makomar nahiyar. Domin kuwa Hausawa su kan ce: „Waiwaye, adon tafiya“.

Ba dai wasu litattafai na tarihi ne zamu karanto ba! Shirin na mu zai duƙufa ne kan wata matashiya da ake kira Julie mai son neman sani. Tare da taimakon kakanta ta shiga binciken tarihin nahiyar tasu.

Sauti da bidiyo akan labarin