1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau za´a sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin kawance a Jamus

November 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvKa

Watanni biyu daidai bayan zaben ´yan majalisar dokokin Jamu ta Bundestag a yau juma´a shugabannin jam´iyu CDU, CSU da SPD zasu rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin kawance. Shugabar CDU Angela Merkel da takwaranta na CSU Edmund Stoiber da kuma sabon shugaban SPD Matthias Platzeck zasu gabatar da jawabai gabanin an kulla wannan kawance tsakanin jam´iyun da a da ke adawa da juna. A jiya da dare jam´iyun suka warware takaddamar da suke yi game da kasafin kudin shekara ta 2006 da kuma sabon bashin da gwamnatin tarayyar zata ci. Bashin kuwa zai kai na Euro miliyan dubu 41 abin da ya zarta adadin na farko na kimanin Euro mliyan dubu 23. Dalilin wannan kari kamar yadda SPD ta ba da hujja shine saboda tabarbarewar tattalin arziki.