A yau litinin ake ganawa tsakanin Schröder da Belka | Siyasa | DW | 27.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A yau litinin ake ganawa tsakanin Schröder da Belka

An shirya ganawa tsakanin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da takwaransa na Poland Marek Belka a fadar mulki ta Berlin domin bitar dangantakun kasashen biyu

Masu iya magana su kan ce ruwa fa ba ya tsami banza. Wannan shi ne ainifin dalilin ziyarar da P/M kasar Poland ga fadar mulki ta Berlin yau litinin. Muhimmin abin da Marek Belka zai mayar da hankali kansa a lokacin ganawarsa da Schröder shi ne cimma wata daidaituwa a hukumance a game da kudaden diyya da Jamusawan da aka kora daga kasar Poland bayan yakin duniya na biyu ke bukatar ganin an biyxa su akan kadarorinsu da aka kwace a wancan lokaci. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Poland Jan Truszynski ya sikankance cewar za a cimma daidaituwa tsakanin sassan biyu. Ya ce ba shakka Schröder da Belka zasdu cimma daidaituwa wajen kafa wani kwamitin hadin guiwa na kwararrun kasashen biyu domin bitar matsalar da kuma neman bakin zaren warwareta a cikin gaggawa ta yadda kotun Turai zata yi fatali da karar da Jamusawan ke neman daukakawa gabanta domin neman diyya daga kasar Poland. Barazanar daukaka kara gaban kotun ta gurbata yanayin dangantaku tsakanin kasashen biyu. Domin kuwa a kokarinta na mayar da martani majalisar dokokin kasar Poland tayi kira ga P/M Marek Belka da ya nemi dubban miliyoyi na kudaden diyya daga gwamnatin Jamus. Ta la’akari da haka P/Mn, wanda a tsakiyar watan oktoba mai zuwa zai fuskanci kuri’ar amnnan da salon kamun ludayinsa, zai yi bakin kokarinsa wajen ganin an cimma daidaituwa akan wannan takaddama. Bisa ta bakin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Poland Jan Truszynski makollin warware wannan rikici na hannun shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder. Babban abin dake ci wa dukkan shuagabannin biyu tuwo a kwarya shi ne kasancewar kimanin kashi 60% na al’umar Poland na goyan bayan ganin an nemi kudaden diyya daga Jamus sakamakon barnar da kasar tayi wa Poland a zamanin yakin duniya na biyu. Irin wannan ci gaba zai yi tasiri a yakin neman zaben kasar ta Poland, muddin ba a dauki nagartattun matakai na sanin ya kamata domin shawo kan lamarin ba, kamar yadda aka ji daga Marek Cichoki daga cibiyar nazarin dangatakun kasa da kasa, inda ya kara da cewar:

Zaben da za a gudanar a shekara ta 2005 zata taka muhimmiyar rawa, kuma kome na iya faruwa a wannan lokaci, saboda kowane daga cikin jami’an siyasar kasar zai yi bakin kokarinsa wajen lashe wannan zabe kuma hakan na iya kara gurbata yanayin da ake ciki yanzun.

Ga alamu dai a lokacin ganawar tasu Belka da Schröder na fatan kafa wani kwamitin bitar dangantakun kasashen Poland da Jamus a hukumance, kamar yadda aka ji daga bakin mataimakin ministan harkokin wajen Poland Jan Truszynski.