A yau ake fara zaben sabon paparoma
March 12, 2013Talla
Manyan shehunan ɗarigar Katholika 115 daga kasashe 48 za su fara kada kuri'a da nufin zaɓan sabon Paparoma da zai maye gurbin Benedikt na 16 mai murabus. A tarihin baya-bayannan dai babu wani Paparoma da ya samu nasara a zagayen farko na zaben wanda aka sani da Conclave.
Shehunan za su taru ne a wani zaure, inda za su yi ta kada kuri'a har sau huɗu a asirce ako wace rana, har lokacin da aka samu Paparoman da ya yi nassara. Daga cikin 'yan takara da ake kyautata zato za su iya kai labari har da manyan limaman da suka fito daga nahiyar Afirka.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal