A yau ake cika shekara guda da ta da tarzomar birnin Paris | Labarai | DW | 27.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ake cika shekara guda da ta da tarzomar birnin Paris

An tsaurara matakan tsaro a fadin kasar Faransa gabanin bukin zagayowar shekara guda da tarzomar matasa da ta yadu a kasar baki daya. Ministan harkokin cikin gida Nicholas Sarkozy ya yi alkawarin girke ´yan sanda wadanda zasu kare motocin safa safa dake jigila a unguwannin dake wajen birnin Paris. Wannan matakin ya biyo bayan jerin hare hare da aka yi jiya da daddare inda matasa suka bankawa motocin bas guda uku wuta a wasu unguwanni dake wajen babban birnin na Faransa. Ba wanda ya samu rauni a hare haren. A ranar 27 ga watan oktoban bara aka ta ta da wata tarzoma wadda aka shafe makonni 3 ana yi tsakanin matasa da ´yan sanda musamman a unguwannin baki marasa galihu dake fadin kasar ta Faransa. Sama da motoci dubu 10 da gidaje 300 aka cunnama wuta. Tarzomar ta fito da matsalolin da ake fuskanta unguwannin Faransawa masu asali da kasashen Larabawa da na Afirka, fili.