A yar da kwallon mangwaro a huta da kuda | Siyasa | DW | 03.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A yar da kwallon mangwaro a huta da kuda

Babban bankin Jamus ya baiwa shugaban kasa shawarar ya kori Thilo Sarrazin daga mukamin sa saboda manufofi na kyamar baki

default

Thilo Sarrazin da littafin da ya rubuta dake nuna alamu na kyamar baki

Tun daga ranar Litinin da ta wuce, littafin da jami'in babban bankin Jamus, Thilo Sarrazin ya rubuta mai suna: Jamus zata share kanta da kanta, ya shiga kasuwnanin sayar da littafai a wannan kasa. Sai dai tun kafin a gabatar da wannan littafi, Sarrazin ya fada muhawara mai tsanani tare da zargin sa da laifukan nuna kyama ga baki yan ci rani da Yahudawa a kasar ta Jamus. Wannan littafi da ya rubuta da kuma muhawarar da ta biyo baya, sun sanya matsayin sa ya raunana a babban bankin na Jamus, inda ma shugabanin bankin suka nemi a kore shi daga mukamin sa na kasancewa daya daga cikin manyan jami'an sa.

Babban bankin na Jamus, wato Deutsche Bundesbank, ya baiyana aniyar sa ta ganin ya yar da kwallon mangwaro, ya huta da kuda, wato a takaice yace zai raba gari tsakanin sa da Thilo Sarrazin. A wani jawabi da bankin ya bayar a Frankfurt, shugabannin sa sun sanar da cewar zasu nemi shugaban kasa, Christian Wulff ya sallami Sarrazin daga mukamin sa, tun da shike tuni ma aka karbe aiyukan da yake tafiyarwa a bankin. Babban bankin yace dalilin daukar wannan mataki, mai tsanani, wanda shine karo na farko da aka taba yin haka a Jamus, shine jawaban da Sarrazin yayi a game da zaman baki da rayuwar su a nan Jamus. Sarrazin, dan jam'iyar siyasa ta SPD, yayi korafin cewar baki basa nuna alamar sajewa da rayuwa a Jamus, kuma yace jinsin Yahudawa suna a wani yanayi na rayuwa da ya maida su duk irin su daya.

Yan siyasa a Berlin sun baiyana farin cikin ganin babban bankin na Jamus zai rabu da ma'aikacin sa Sarrazin, wanda mutum ne da yayi kaurin suna wajen jawabai na kyamar baki da yanayin rayuwar baki da neman sajewar su a Jamus, inda kuma a duk lokacin da yayi irin wadannan jawabai, sukan haddasa bacin rai da bakin ciki mai tsanani. Lokacin zaman wani taro na babban bankin, wanda shi kansa Sarrazin bai halarta ba, shugaban bankin, Axel Weber ya fadi a Frankfurt cewa:

"Hukumar gudanarwa ta babban bankin a yau ta yanke kudirin mika bukata ga shugaban kasa, domin ya sallami Thilo Sarrazin daga mukamin sa na daya daga cikin shugabanin wannan banki. Mun yanke wannan kudiri ne ba tare da hamaiya ba, kuma duka bakin mu yazo daya a kan wannan al'amari".

To sai dai babban bankin bai gabatar da dalilan dauka wannan mataki a bainar jama'a ba. Shugaban kasa, Christian Wulff yanzu dai shawara ta karshe ta rage gareshi, inda ya sanar da cewar zai yi nazarin wannan bukata, kuma zai yanke kudirin da yake ganin ya dace. Duk da haka, shi kansa shugaban kasar tun da can ma, a kaikaice ya baiwa bankin shawarar ya rabu da Sarrazin.

Shugaban gwamnati, Angela Merkel tace ko ba tare da ta kula da kudirin da shugabannin babban bankin suka gabatar ba, amma tana marhabin da wnanan mataki. Tun da farko sai da ta nuna cewar kokarin da Sarazin yake yi na haddasa fitina al'amari ne da bai dace ba.

"Tace batun zaman baki da daidaita rayuwar su a tsakanin su, al'amari ne babba. Mun yi gagarumin aiki dangane da haka, kuma zamu ci gaba da yin gagarumin aiki game da hakan. To amma irin yadda ake ta magana kan wannan al'amari a yanzu, abu ne da zai kawo rarraba kan jama'a, tare da sanya muhawarar da ake yi ta kara zama mai wahala".

Shugaban babban bankn Israila, Stanley Fischer yayi magana da takwaran aikin sa na Jamus, Axel Weber, inda ya baiyana gamsuwar sa kan matakin koran Sarrazin daga mukamin sa.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Abdullahi Tanko Bala