A Siriya agaji ya isa yankuna da ke killace | Labarai | DW | 02.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Siriya agaji ya isa yankuna da ke killace

Kungiyar agajin gaggawa ta Red Cross ta tabbatar cewa a jiya tawagar motocinsu dauke da magani da alluran riga kafi da abinci, sun shiga birnin Daraya da ke kasar, wanda aka killace shi tun shekara hudu da suka gabata.

MDD ta yi gargadin cewa yara dake rayuwa a birnin na Daraya da aka killace na gab da mutuwa bisa rashin abinci mai gina jiki. Shi kuwa kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka John Kirby ya fadawa manema labarai cewa.

"MDD da kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross hade na kasar Siriya, sun tabbatar da isa garin na Daraya da kuma garin Mouadhimiyeh. Kai agaji ta kasa shi ne kawai zabin da ya rage, mai amfani ga samarwa mutanen tallafi a yankunan da aka killace. Ko da yake an samu nasarar kai agajin na jiya, amma akwai sauran jan aiki a wajen samar da tallafi ga dubban Siriyawa da ke matukar bukata"

Kasar Rasha dai ta sanar da dakatar da bude wuta a birnin na tsawon kwanaki biyu, yayin da 'yan tawaye ke cewa kamata ya yi a tsawaita dakatar bude wuta izuwa wata daya wato har a kare azumin watan Ramadan