A Saliyo cutar Ebola ta shiga fadar gwamnati | Labarai | DW | 01.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Saliyo cutar Ebola ta shiga fadar gwamnati

Mataimakin shugaban kasar Saliyo da kansa a yanzu ya koma sansanin da ake kebe wa masu cutar Ebola, bayan da daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa ya mutu daga cutar.

Wannan labarin da ya fito daga ofishin Samuel Sam-Sumana maitamakin shugaban kasar ta Saliyo, ya mai da hannun agogo baya bisa murnar da aka yi a yaki da cutar, inda ta kai ga har gwamnati ta sake bude makarantun kasar, bisa fatan an shawo kan cutar ta Ebola. To amma a halinda ake ciki, gwamnati ta maido da daukar tsauraren matakai na hana zirga-zirga, bayan samun tabbacin kwayar cutar Ebola na buzuwa. An dai fi mayar da hankali ne kan masu kai-kawo da jiragen kwale-kwale a gabar tekun kasar. Kawo yanzu dai sama da mutane 9,500 suka mutu sakamakon cutar ta Ebola, tun bayan bullarta a kasar Gini shekara daya da watanni.