A Najeriya mazauna Garkida na neman dauki | Labarai | DW | 22.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Najeriya mazauna Garkida na neman dauki

Bayan hari da 'yan bindiga suka kai garin Garkida da ke karamar hukumar Gombi a jihar Adamawa ta Najeriya, har yanzu ana cikin zulumi gami da neman dauki na tsaro.

Mazaunan a garin na Garkida sun tabbatar da kone-kone da 'yan bindigar da ake zargin na Boko Haram ne suka yi ciki har da majami'u da gidajen fitattun 'ya'yan yankin.

Rahotanni na cewa mazauna garin na Garkida na cikin hali na dar-dar, bayan harin da 'yan bindiga suka kansu a ranar Juma'a.

Wani mazaunin garin, Manu Usman Bakari, wanda a ya tsare da iyalinsa, ya yi wa DW bayani tare da tabbatar da mutuwar wasu jami'an tsaro.

Galibin jamaa dai sun kaurace wa garin, saboda fargabar abin da ka yia kasancewa. An kuma kokawa kan rashin kasuwanni da shagunan sayar da magunguna.