A Najeriya kwamitin taron ƙasa ya fara aiki | Siyasa | DW | 07.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A Najeriya kwamitin taron ƙasa ya fara aiki

Shugaba Goodluck Jonathan ya ƙaddamar da kwamitin da aka ɗorawa alhakin nazarin tattauna makomar ƙasar.

Nigerianischer Präsident Goodluck Ebele Jonathan mit Mitgliedern des Komitees zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz in Nigeria Bild: Korrespondent Ubale Musa

Shugaba Jonathan da 'yan kwamitin tattauna shirya taron kasa

An dai kai ga girka kwamitin bayan sanarwa da shugaban ya bayyana a makon jiya ta yi taron na ƙasa. Kuma ana shirin tabbatar da ganin sakamako a cikin gwagwarmayar neman mafita ga makomar Tarayyar Najeriya, da ta share shekaru har 53 na yancin kai ta na kwan -gaba, kwan -baya. Wani jawabin shugaban ƙasar na ranar yanci dai ya kai ga bude sabon babi a cikin ƙoƙarin samar da samuwar makoma ga ƙasar da ta fara sabuwar tafiya cikin wasu shekaru 50 na kan gaba cikin hali na ruɗani da rashin tabbas.

Ignatius Kaigama, Erzbischof von Jos/Nigeria Wer hat das Bild gemacht?: Thomas Mösch, DW Wann wurde das Bild gemacht?: 13.06.2011 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Jos/Nigeria Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Ignatius Kaigama, katholischer Erzbischof von Jos, Plateau State, Nigeria

Ignatius Kaigama, shugaban majalisar manyan limaman Katholika a Najeriya

Taron na ƙasa da nufin tattaunawa a fadar shugaba Jonathan da ya kai ga ƙaddamar da sabon kwamitin nazarin hanyoyin tattaunawar dai ne mafita, ga jerin ƙalubale na siyasa da ma zamantakewar.

"A gare ni ba wani abun da ya wuci jin ra'ayin kowa da daidaito da kuma adalci a cikin sabon tsarin demokraɗiyyar mu. Ina son in yaye tsoro a zukata na masu ganin ta zo ƙarshe ga ƙasar. Maimakon haka tattaunawar na zaman sabuwar dama ta ƙara ƙarfi na haɗin kai, da kuma warware matsalolin da suke da muhimmanci, amma kuma ake manta wa da su kusan ko wane lokaci."

Sultan Sa'ad Abubakar III. Stichworte: Nigeria, Sultan, Sa'ad Abubakar III., Sokoto Sa'ad Abubakar III. ist seit 2006 Sultan von Sokoto und damit spirituelles Oberhaupt der Muslime in Nigeria. Offizielles Foto, copyright: Sultan's Office

Sa'ad Abubakar III. Sarkin musulman Najeriya

Kama daga malamai na addini ya zuwa masu sana'a ta siyasa dama masu gani ba kyale wa dai, tun ba'a kai ko ina ba dai kwamitin ya fara ganin fasara iri-iri, da suka hada da ƙoƙarin dora ƙasar bisa wani sabon nau'in rikici ya zuwa na cewar shiri ne da ke ɗaukar hankali a ɓangaren gwamantin. To sai dai kuma kwamitin da shugaban ya kara wa'adin aikinsa zuwa makonni har shida dai, a cewar Dr Abubakar Sadiq da ke zaman ɗaya daga cikin yayansa, ba zai zamo kafa ta amshin shata ga gwamanti.

Samar da damar raba Najeriya ko kuma ƙoƙarin a ƙara mata ƙarfi dai, ƙalubale na farko a gaban yan kwamitin mai wakilansa 13, na zaman samun karbuwar batutuwan da suke shirin tsarawa ga ƙasar da tuni ra'ayi ke rabe kan hanyoyin neman mafitar warware rigingimun kasar ta Najeriya.

Pupils of preliminary school in Abuja, Nigeria. (10.03.2009). Foto: LEHTIKUVA / Antti Aimo-Koivisto +++(c) dpa - Report+++

Yara manyan gobe, a Najeriya

Tun ba'a kai ko ina ba dai alal misali wasu sassan ƙasar suka fara kiran kai wa kasuwa game da tsoma baki da taka rawarsu cikin taron da ke zaman irinsa na farko da gwamantin ta ce ba shi da shamaki kan komai. To sai dai kuma a faɗar gwamna Ibrahim Shehu Shema da ke zaman gwamnan jihar Katsina, ƙasar yace ba shi da sha'awa ga tattauna halin lamuran ƙasar ta Nageriya na yanzu.

kama daga taron gyara kundin tsarin mulkin ƙasar na shekara ta 1978 ya zuwa ɗan uwansa na shekara ta 1987, dama wanda ya biyo baya a shekara ta 1995, kafin na tsohuwar gwamnatin Chief Olusegun Obasanjo a shekara ta 2006, 'yan ƙasar dai sun kai ga kallon siddabru iri-iri a ƙoƙarin dora ƙasar bisa tafarkin mulki na gari, tun bayan yancin kan na ta na shekara ta 1960.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin